Manyan Abubuwa 3 da Gwamnatin Tinubu Ta Fusata Mutanen Arewa da Su

Manyan Abubuwa 3 da Gwamnatin Tinubu Ta Fusata Mutanen Arewa da Su

Watan Oktoba da ta gabata ta zo wa Arewacin Najeriya da manyan kalubale da su ka jawo asarar rayuka, kudi da kuma jefa mazauna yankin a cikin zullumi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Mazauna Arewacin kasar nan sun shiga mawuyacin hali bayan shafe fiye da rabin Oktoba babu wutar lantarki, wanda kungiyar kare hakkin dan Adam ta IHRC ta ce an yi asarar sama da N1.trn.

Arewa
Abubuwa 3 da su ka addabi Arewa a watan Oktoba Hoto: Bayo Onanuga/Sanusi Bature/Transmission Company of Nigeria
Asali: Facebook

A wannan rahoton, Legit ta tattaro manyan abubuwa uku da su ka jefa Arewacin Najeriya a cikin tsanani a watan Oktoba, wanda wasu ke shafar jama'a har yanzu.

1. Katsewar hasken lantarki zuwa Arewa

Kara karanta wannan

Band A: Masu samun wutar awa 20 a rana sun gaji, sun kai kuka wajen Tinubu

Tun a ranar 9 ga watan Oktoba hasken lantarkin Arewacin Najeriya ya samu matsala, kuma an shafe akalla sati uku ba a samu gyara hasken wutar ba bisa wasu dalilai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Channels Television ta wallafa cewa kamfanin hasken lantarki kana TCN ya nanata yadda ake zargin yan bindiga da kawo cikas a wajen gyaran lantarkin shiyyar.

Kungiyoyi kamar su 'Jino Foundation' da 'Internation Human Rights Commission' sun shaidawa Legit cewa an tauye hakkin jama'a, domin an tafka asarar akalla N1.trn.

Sai dai an ji shugaban kasa, Bola Tinubu ya bayar da umarni ga Minisan makamashi, Adebayo Adelabu da ya tabbata an sada Arewa da haske, lamarin da yanzu ba lallai ya yiwu ba ganin cewa kasar na fada a cikin duhu.

2. Gwamnatin Tinubu ta maka yaran Arewa kotu

Hankalin musamman mazauna Arewacin kasar nan ya tashi matuka bayan bullar bidiyon yara masu karancin shekaru da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta maka a gaban kotu bisa zargin cin amanar kasa.

Kara karanta wannan

Ba a gama da Kano ba, gwamnatin Zulum ta gurfanar da kananan yara da wasu 16

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa jam'ar kasar nan sun gudanar da zanga zanga ta kwanaki 10 da aka fara a ranar 1 Agusta, 2024 saboda adawa da yunwa, kuma an samu asarar rayuka a lokacin,

Bayan fara zanga zanga ne aka samu wasu matasa su ka rika daga tutar Rasha su na neman a agaza masu, wannan ta sa aka fara kama matasa tare da tsare su a hannun DSS ko yan sanda.

A ranar Juma'a 1 Nuwamba ne gwamnatin Tinubu ta gurfanar da yaran a gaban kotu wanda ya harzuka manyan kasar nan ciki har da Atiku Abubakar, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Facebook.

A ranar Talata, 10 Nuwamba, 2024 kuma kotu ta kori karar da gwamnatin ta shigar bayan shugaban kasa, Bola Tinubu ya bayar da umarnin janye tuhumar da ake yi wa yaran.

Gwamnatin jihar Kano ta yi wa yaranta da su ke cikin wadanda aka kama uwa da makarbiya, inda ta tura tawaga Abuja aka kuma dawo da yaran jihar Kano domin sada su da iyayensu.

Kara karanta wannan

Rashin lantarki: An fara haɗa alkaluman asarar Arewa, za a nemi diyya daga Tinubu

3. Gwamnonin Arewa sun fusata da tsarin haraji

Gwamnonin Arewacin kasar nan sun hada baki a wajen fatali da sabon tsarin harajin da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya bijiro da shi.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa gwamnonin su na ganin abubuwan da sabon kudurin harajin ya kunsa ba zai yi wa Arewa da mazauna shiyyar dadi ba, kuma su ka nemi a janye ta.

A martanin gwamnatin tarayya, babu abin da zai sa a janye sabon tsarin harajin domin ba a bijiro da shi domin muzantawa kowa ba.

Sai dai akwai Sanatoci irinsu Muhammad Ali Ndume, wanda ya bayyana cewa ba za su amince da tsarin harajin da Tinubu ke son kakabawa yan Najeriya ba.

Gwamnatin Tinubu ta tarbi yaran Arewa

A baya mun ruwaito cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta tarbi yaran da ta daina shari'a da su a Aso Rock jim kadan bayan kotu ta kori shari'ar bisa janye tuhume tuhumen da gwamnati ta yi.

Kara karanta wannan

Rashin lantarki: Yan Arewa sun tafka asara, an rasa sama da Naira tiriliyan 1

Bayan tarbar yaran ne aka ji mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima na cewa Tinubu a bayar da umarnin sakin kananan yaran ne saboda tausayi irin wanda shugaban ke da shi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.