Ba a Gama da Kano ba, Gwamnatin Zulum Ta Gurfanar da Kananan Yara da Wasu 16
Borno - Rundunar ‘yan sanda ta gurfanar da wasu mutane 19 da suka hada da kananan yara 3 a gaban wata babbar kotun jiha da ke Maiduguri, jihar Borno.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake matsin lamba ga gwamnatin tarayya da ta janye tuhumar da ake yi wa kananan yara da aka kama kan zanga-zangar tsadar rayuwa.
An gurfanar da kananan yara a Borno
A Borno, an gurfanar da mutane 16 a gaban Mai shari’a Aisha Mohammed Ali bisa zargin su da hannu a zanga-zangar watan Agusta, inji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar takardar tuhumar da aka shigar, kananan yaran uku suna tsakanin shekaru 14 zuwa 17.
An rahoto cewa gwamnatin jihar Borno ce ta yi karar wadanda ake tuhumar a gaban kuliya bisa tuhume-tuhume da suka shafi cin amanar kasa.
Sauran zargin sun shafi amfani da kafafen sada zumunta wajen bata sunan gwamnan jihar da kuma tunzura jama’a a kan jihar.
Bayanin laifuffukan da yaran suka aikata
A cewar masu gabatar da kara na jihar, kananan yaran suna daga cikin mutane bakwai da suka hada baki domin bude dandali mai suna 'Zanga-zanga' a Whatsapp da Tiktok.
An ce yaran sun amince a tsakaninsu cewa za su dauki makamai domin yakar gwamnatin jihar, wanda ya ke da hukunci a sashe na 79 na dokar 'Penal Code' ta jihar Borno, 2023.
An tuhumi mutane 11 da laifin daga tutar Rasha a bainar jama'a, wanda ya sabawa sashe na 42 da hukunci a karkashin sashe na 76(b) na dokar Penal Code ta jihar.
Sai dai a lokacin da aka karanta wa wadanda ake zargi tuhume-tuhumen, dukkansu sun musanta aikata laifuffukan.
Tinubu ya umarci a saki yaran Arewa
A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaba Bola Tinubu, ya yi magana kan yaran da aka tsare tare da gurfanar da su a gaban kotu saboda zanga-zanga.
Shugaba Tinubu ya ce a gaggauta sakin dukkanin yaran da aka kama kuma aka gurfanar da su gaban kotu bisa zarginsu da hannu a zanga-zangar adawa da gwamnati.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng