Matsala Ta Kunno Kai a Kano, Takardun Naira Sun Fara Ƙaranci a Hannun Jama'a

Matsala Ta Kunno Kai a Kano, Takardun Naira Sun Fara Ƙaranci a Hannun Jama'a

  • Matsalar ƙarancin kudin Najeriya watau Naira ta kunno kai a jihar Kano kuma tana neman zama barazana ga harkokin kasuwanci
  • Mazauna Kano da masu sana'ar POS sun koka kan rashin wadatar takardun Naira, inda suka ce lamarin ya shafi harkokin yau da kullum
  • Wani mai POS ya ce ga dukkan alamu su kansu bankuna sun fara rasa tsabar kudi saboda yadda suka daina ba su adadin da suka buƙata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Rahotanni daga jihar Kano a Arewa maso Yammacin Najeriya na nuna cewa mutane sun fara shiga matsalar karancin takardun Naira.

Mazauna birnin Kano, cibiyar kasuwanci a Arewa sun fara nuna damuwa kan karancin kudi a hannu a ƴan kwanakin nan.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sake kai mummunan hari, sun kashe bayin Allah ta hanya mai muni

Takardun Naira.
An fara karancin takardun Naira a jihar Kano Hoto: Contributor
Asali: Getty Images

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa matsalar karancin kudin ya fara barazana ga kasuwanci da kuma harkokin al'umma na yau da kullum.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƙarancin Naira: Mutanen Kano sun koka

Wani bakano, Halliru Akilu ya ce a halin da ake ciki yanzu samun tsabar kudi ya yi wahala hatta a wurin masu POS ba a cika samu ba.

Mutumin ya ce:

"A gaskiya ana ƙarancin takardun kudi kwanan nan, ni ban saba fitowa da kudi a jikina ba, sai na fito nake zuwa wurin masu POS na cira, amma yanzu abin ya yi wahala.
"Idan ka je wurin masu POS bai wuce ka samu N1,000 ko N2,000 ba, shi ma sai ka yi da gaske, zuwa wurin aiki ya zama abu mai wahala, ba su karɓar tiransufa, dole ka nemi kudi."

Bisa haka Halliru ya yi kira ga gwamnati da hukumomin da abin ya shafa su duba lamarin domin yana shafar harkokin kasuwanci da rayuwar yau da kullum.

Kara karanta wannan

Wani bom ya tarwatse da mutane a babbar kasuwa a Najeriya, an rasa rayuka

"Babu tsabar kudi a bankuna" - Mai POS

Haka nan wani mai POS, A. A Adamu, ya koka kan yadda mutane musamman ‘yan kasuwa suka dena kai kudadensu bankuna, sun gwammace yin mu’amala da tsabar kudi.

"Watanni biyu kenan muna fama da wannan matsalar, su kansu bankuna yanzu ba su samun tsabar kuɗin daga CBN, idan ka nemi N500,000 bai wuce su ba ka N30,000," in ji shi.

Wani ɗan Kano, Malam Aminu Suleiman ya shaidawa Legit Hausa cewa da yiwuwar akwai karancin kudi amma ba a ko ina ba.

Aminu ya ce kullum idan ya baro gida yana zuwa wurin wani mai POS ya cire kudin da zai yi amfani da su.

Ya ce:

"Eh to da yiwuwar hakan a wasu wuraren, kullum ina cire N20,000 a POS a Unguwarmu Mil 9, to amma jiya ya faɗa mani babu sai ya nemo, ban ɗauki hakan da wata matsala ba.

Kara karanta wannan

Sabuwar kungiyar yan ta'adda na raba miliyoyi domin rudar matasan Arewa

"Yau kamar yadda na saba na je kuma na cire, wataƙila ni da nake zuwa kullum ba a gaya mun halin da ake ciki ba. Muna fatan Allah ya warware mana."

Majalisa ta umarci a janye tsofaffin Naira

A wani rahoton, kun ji cewa majalisar wakilai ta ba babban bankin Najeriya (CBN) umarnin janye tsofaffin takardun Naira daga hannun jama'a.

Bayan wani kudurin gaggawa da Hon. Adam Victor Ogene ya gabatar, majalisar ta umarci bankin CBN ya wadatar da sababbin kudi a kasar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262