'Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari kan Ofishin Ƴan Sanda, an Kashe Mutum

'Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari kan Ofishin Ƴan Sanda, an Kashe Mutum

  • Kwamishinan 'yan sandan jihar Abia, Danladi Isa ya tabbatar da cewa 'yan bindiga sun farmaki ofishin 'yan sandan Owerrinta
  • Danladi Isa ya ce 'yan bindigar sun dura ofishin kan motoci uku inda suka yi amfani da abin fashewa wajen fasa rufin ofishin
  • A yayin artabu da jami'an 'yan sanda, kwamishinan ya ce an samu akasi inda aka kashe wata mata da aka tsare a cikin ofishin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abia - A ranar Litinin ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari a ofishin ‘yan sandan RSS da ke Owerrinta, kan babbar hanyar tarayya ta Umuahia zuwa Aba.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kwamishinan ‘yan sandan jihar, Danladi Isa, ya ce an kama mutum daya daga cikin wadanda ake zargi da kai harin.

Kara karanta wannan

Ba a gama da Kano ba, gwamnatin Zulum ta gurfanar da kananan yara da wasu 16

Rundunar 'yan sanda ta yi magana kan harin da 'yan bindiga suka kai ofishinta na Abia
Abia: 'Yan bindiga sun kai hari ofishin 'yan sandan RRS, an kashe mutum 1. Hoto: @Princemoye1
Asali: Twitter

Jaridar Punch ta rahoto cewa 'yan bindigar sun harbe wata mata da ake tsare da ita a cikin ofishin 'yan sanda kuma ta mutu nan take.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan bindiga sun farmaki 'yan sanda

Danladi Isa ya bayyana cewa:

“A wannan ranar, an kai hari a ofishinmu da ke Owerrinta wajajen Asubah. 'Yan bindigar sun isa ofishin a kan motoci kilar Hilux uku inda suka bude wuta.
“Jami’anmu sun dakile harin. Sai dai kuma, 'yan ta'addan sun yi amfani da abin fashewa wajen fasa rufin ofishin.
A yunkurinsu na kubutar da wasu fursunoni, sun bude wuta, lamarin da ya yi sanadin mutuwar wata mata da ake zargi da kisan gilla.”

Matakin da 'yan sanda suka dauka

Bayan afkuwar lamarin, kwamishinan 'yan sanda ya ce sun bi diddigin wadanda ake zargin ta hanyar amfani da fasaha inda suka yi nasarar cafke mutum guda.

Kara karanta wannan

Dillalan mai 4 sun shigo da fetur na N833bn yayin da Dangote ya fadi farashinsa

"Yanzu haka dai ‘yan sanda na ci gaba da yi masa tambayoyi domin gano sauran wadanda suka aikata laifin. Muna samun ci gaba.”

- A cewar Danladi Isa.

Rahotannin da ba a tabbatar da su ba sun nuna cewa an tsare matar da aka kashe a lokacin harin bisa zargin tana safarar kananan yara.

'Yan bindiga sun farmaki 'yan sanda

A wani labarin, mun ruwaito cewa 'yan bindiga sun farmaki ofishin 'yan sandan Ohaukwu da ke Ezzamgbo, hedikwatar karamar hukumar Ohaukwu a jihar Ebonyi.

An ce jami'an 'yan sandan da ke bakin aiki a ofishin sun yi musayar wuta da 'yan bindigan, inda aka kona motocin jami'an tsaron da lalata wasu kadarori.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.