'Ku bar Zagin Shugabanni': Sultan ga Yan Najeriya, Ya Ja Kunnen Malaman Addini

'Ku bar Zagin Shugabanni': Sultan ga Yan Najeriya, Ya Ja Kunnen Malaman Addini

  • Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar III ya shawarci al'umma kan sukar shugabannin da ke mulki a Najeriya
  • Sultan ya ba yan kasa shawara da su bar zagin shugabanni domin kowa zai girbi abin da ya shuka ranar gobe kiyama
  • Mai alfarma ya kuma gargadi malamai da su yi hankali wurin karantar da mabiyansu domin wata bukatar kansu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna - Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar III ya ja kunnen al'umma kan zagin shugabanni.

Sultan ya shawarci yan Najeriya da su cigaba da yi wa shugabanni addu'a da kuma kasar Najeriya gaba daya.

Sarkin Musulmi ya ja kunnen yan Najeriya kan zagin shugabanni
Sarkin Musulmi, Sa'ad Abubakar ya ba yan Najeriya shawara kan yiwa shugabanni addu'a. Hoto: Sultan Sa'ad Abubakar.
Asali: Facebook

Sarkin Musulmi ya magantu kan halin shugabanni

Mai Martaba ya ce ya dace a bar shugabannin da Ubangiji ya yi yadda zai yi da su, cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta fara shirin janye zarge zarge kan yara 32 a gaban kotu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sultan ya ce babu wani abu mai kyau ko marar kyau da zai tabbata a duniya inda ya shawarci gudanar da addu'o'i ga kasa.

Basaraken ya kuma tunatar da shugabanni ranar karshe inda ya ce babu mai cetonsu daga su sai abin da suka aikata.

Sultan ya gargadi malaman addini kan koyarwa

Sarkin Musulmi ya gargadi malaman addini kan kidimar da mabiyansu domin biyan buƙatar kansu, Vanguard ta ruwaito.

Sultan ya ce mafi yawan al'ummar suna amincewa da malamansu a masallatai ko coci saboda yadda suke mutunta su.

"Mutane da dama suna cewa ba a taba samun matsala irin yanzu ba, amma kuma komai ya yi zafi za a samu sauki."
"Mun yi imani babu wani abu da zai tabbata, ya kamata mu rinka nunawa mabiyanmu su yiwa shugabanni addu'a."
"Bai kamata mu rika zagin shugabanni ba, mu bar su da Allah ya yi yadda ya ga dama da su."

Kara karanta wannan

Pantami da mutane sun fusata da maka kananan yara a Kotu saboda zanga zanga

- Sarkin Musulmi

Farfesa Pantami ya samu sarauta a daular Usmaniyya

Kun ji cewa Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar III ya ba Farfesa Isa Ali Pantami da sarauta a daular Usmaniyya.

Sultan Muhammad Sa'ad ya ba Farfesa Pantami sarautar Majidadin Daular Usmaniyya a ranar Asabar 2 ga watan Nuwambar 2024.

Wannan ya biyo bayan gudanar da taron shekara na Sheikh Usman dan Fodiyo karo na 11 da aka saba yi a jihar Sokoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.