Rikicin Kwallon Kafa: 'Yan Najeriya Mazauna Libiya na Fuskantar Tsangwama?

Rikicin Kwallon Kafa: 'Yan Najeriya Mazauna Libiya na Fuskantar Tsangwama?

  • Ma'aikatar harkokin waje ta karyata jita jitar da ake yadawa kan cewa ana cafkewa tare da azabtar da 'yan Najeriya a kasar Libiya
  • Ma'aikatar, karkashin minista Yusuf Tuggar ta ce 'yan Najeriya na gudanar da harkokinsu a Libiya ba tare da wata tsangwama ba
  • Martanin ma'aikatar na zuwa ne yayin da rahoto suka fara karade intanet cewa ana cin zarafin 'yan Najeriya bayan hukuncin CAF

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Ma'aikatar harkokin wajen Najeriya ta yi martani kan rahoton da ke yawo cewa 'yan ƙasar nan mazauna Libiya ba sa fuskantar tsangwama.

Ma'aikatar wadda ke karkashin ministan harkokin waje, Yusuf Tuggar ta ce ko kadan, babu wani dan Najeriya da ke fuskantar takura a Libiya.

Kara karanta wannan

Band A: Masu samun wutar awa 20 a rana sun gaji, sun kai kuka wajen Tinubu

Najeriya ta yi magana kan zargin tsangwamar da 'yan kasarta ke fuskanta a Libiya
Gwamnatin Najeriya ta karyata jita jitar cin zarafin 'yan Najeriya a Libiya. Hoto: @CAF_Online, @NGSuperEagles, @LibyaReview
Asali: UGC

Zarge-zarge bayan hukuncin hukumar CAF

A watan Oktoba ne Najeriya ta yi zargin cewa an wulakanta tawagar Super Eagles a filin jirgin sama na Al Abaq da ke Libiya inji rahoton The Cable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan bincike, hukumar kwallon kafar Afrika (CAF) ta ci tarar Libiya $50,000 sannan ta ba Najeriya kyautar maki uku da kwallaye uku.

Biyo bayan wannan hukunci, an samu rahotonni da suka nuna cewa 'yan Libiya na cin zarafi da kuma nuna tsangwama ga 'yan Najeriya mazauna kasar matsayin ramuwar gayya.

Wane hali 'yan Najeriya ke ciki a Libiya?

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa, ma'aikatar harkokin wajen Najeriya a ranar Lahadi, ta karya zargin cewa ana cin zarafin 'yan Najeriya a Libiya.

A cikin wata sanarwa da ma'aikatar ta fitar, ta ce 'yan Najeriya na kan gudanar da rayuwarsu ta yau da kullum a Libiya ba tare da fargaba ko tsangwama ba.

Kara karanta wannan

Matsala ta kunno kai a Kano, takardun Naira sun fara ƙaranci a hannun jama'a

"Ma'aikatar harkokin waje ta karyata ikirarin cewa ana cafke 'yan Najeriya tare da cin zarafinsu a Libiya sakamakon hukuncin da hukumar CAF ta yanke."

- A cewar sanarwar.

Super Eagles ta dawo gida daga Libiya

A wani labarin, mun ruwaito cewa tawagar Super Eagles ta sauka a filin sauka da tashin jiragen sama na Aminu Kano da ke birnin Kano daga kasar Libiya.

An rahoto cewa tawagar ta Najeriya ta je Libya ne domin buga zagaye na biyu a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin Afirka amma aka samu matsala, aka fasa wasan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.