"Cin Mutunci ne": Jagora a PDP Ya Soki Tsare Yara saboda Zanga Zanga

"Cin Mutunci ne": Jagora a PDP Ya Soki Tsare Yara saboda Zanga Zanga

  • Cif Olabode George ya fito ya yi Allah wadai da tsare ƙananan yara saboda shiga zanga-zanga #EndBadGovernance
  • Jigon na jam'iyyar PDP ya bayyana matakin a matsayin cin mutunci kuma abin kunya da tsabagen mugunta
  • Ya bayyana cewa bai kamata a ce shugaban ƴan sandan Najeriya ya bari an yi musu cin mutuncin da suka fuskanta ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Legas - Wani jigo a jam’iyyar PDP, Cif Olabode George, ya yi Allah-wadai da gurfanar da yaran da aka tsare saboda zanga-zanga a gaban kotu.

Gurfanar da yaran da aka yi a gaban kotu ya jawo mutane sun yi ta tofin Allah tsine tare da nuna ɓacin ransu kan hakan.

Kara karanta wannan

2027: Tsohon hadimin shugaban ƙasa ya faɗi ma'anar sunan 'T-Pain' da ake kiran Tinubu

Bode George ya caccaki tsare yara
Bode Goerge ya Allah wadai da tsare yara Hoto: Omoyele Sowore, Olabode George
Asali: Facebook

Bode George ya soki tsare yaran da aka yi ne yayin wata hira da jaridar The Punch a ranar Lahadi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jigon PDP ya soki kai yara kotu

Jagoran na PDP ya caccaki lamarin wanda ya bayyana a matsayin abin ƙyama, cin mutunci kuma abin kunya.

Bode George ya bayyana cewa kamata ya yi shugaban ƴan sandan Najeriya ya ɗauki matsaya wajen nemo hanyar da za a hukunta su maimakon wannan cin mutuncin da aka yi musu.

"Tabbas abin ƙyama ne, tsabagen mugunta ce. Waɗannan yaran masu ƙananan shekaru ne. Idan da ƴan uwansu ne za su yi musu haka?"
"Abin kunya ne, ta ya ya muka zama mugaye haka? Mun bar duk wani halin kamala da mutuntaka."
"Meyasa IGP bai umarci wani ya soke abin da aka yi musu ba, sai da aka tsare su sannan aka gurfanar da su a kotu, to me za su yi? Ba mu da kotun ƙananan yara ne? Wai me yake faruwa ne?"

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya dauki mataki kan yaran da aka tsare saboda zanga zanga

"Na yi Allah wadai da hakan kuma zan ci gaba da yi. Wannan cin mutunci ne."

- Bode George

Matasa sun fusata kan tsare yara

A wani labarin kuma, kun ji cewa wata ƙungiyar Arewa ta ‘National Youth Alliance ta caccaki gwamnatin Bola Ahmed Tinubu game da gurfanar da kananan yara a gaban kotu.

Ƙungiyar, karkashin jagorancin shugabanta na kasa, Aliyu Bin Abbas ta kwatanta yadda gwamnati ta tsare yaran da tsare da garkuwa da mutane.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng