Bayan Kamun Hukumar EFCC, Bobrisky Ya Tsere daga Najeriya

Bayan Kamun Hukumar EFCC, Bobrisky Ya Tsere daga Najeriya

  • Shahararren dan daudu mai suna Idris Okuneye da aka fi sani da Bobrisky ya samu damar ficewa daga tarayyar Najeriya
  • Idris Okuneye ya fita daga Najeriya ne bayan ya yi yunkurin fita daga kasar har sau biyu ba tare da samun nasara ba
  • A makon da ya wuce ne hukumar EFCC ta cafke Bobrisky a filin jirgin saman Murtala Muhammad yana shirin tafiya London

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shahararren dan daudun Najeriya, Idris Okuneye da aka fi sani da Bobrisky ya samu fita daga Najeriya.

A baya, Bobrisky ya yi yunkurin fita daga Najeriya har sau biyu inda hukumomin kasar suke cafke shi.

Kara karanta wannan

Rikicin kwallon kafa: 'Yan Najeriya mazauna Libiya na fuskantar tsangwama?

Bobrisky
Bobrisky ya fice daga Najeriya. Hoto: Bobrisky
Asali: Instagram

Jaridar Punch ta wallafa cewa Bobrisky ya yi alfahari kan kudin jirgi da ya kashe yayin fita daga tarayyar Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda EFCC ta kama Bobrisky a Legas

A makon da ya wuce ne hukumar EFCC ta kama Bobrisky a filin jirgin saman Murtala Muhammad a Legas yana shirin tafiya London.

Haka zalika jami'an shige da ficen Najeriya sun taba kama Bobrisky a iyakar Najeriya da kasar Benin yana shirin fita waje.

Bobrisky ya tsere daga Najeriya

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Idris Okuneye da aka fi sani da Bobrisky ya samu nasarar ficewa daga Najeriya.

Wannan shi ne karo na uku da Bobrisky ya yi yunkurin fita daga Najeriya tun bayan kamun da EFCC ta masa kan cin zarafin takardun Naira.

Wace kasa Bobrisky ya tafi daga Najeriya?

Dan daudun bai bayyana kasar da ya tafi ba sai dai ya sanar da cewa ya biya kudin kujerar jirgi mai tsada inda ya kashe Naira miliyan 30.

Kara karanta wannan

EFCC ta cafke Bobrisky zai sulale London, ya bukaci taimako

Har ila yau dan daudun ya bayyana cewa fasfo din shi ya samu ƴar matsala ta inda hoton shi bai fito da kyau ba.

Ana sa ran cewa nan gaba kadan Bobrisky zai bayyana kasar da ya tafi ga yan Najeriya a kafafen sada zumunta.

Bobrisky ya amsa shi namiji ne

A wani rahoton, kun ji cewa shahararren dan daudu mai suna Idris Okuneye, da aka fi sani da Bobrisky, ya amsa cewa shi namiji ne.

Dan daudun ya amsa hakan ne a lokacin da mai shari'a Abimbola Awogboro ya tambayesa jinsinsa kafin yanke masa hukunci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng