An Rufe Gidan Rediyo ana Tsaka da Maganar Kananan Yaran Arewa da aka Kai Kotu

An Rufe Gidan Rediyo ana Tsaka da Maganar Kananan Yaran Arewa da aka Kai Kotu

  • An dakatar da ayyukan gidan rediyon Brekete Family da ke fafutukar kare hakkin bil'Adama kan tsare kananan yaran Arewa
  • Shugaban gidan rediyon, Ahmed Isa ya nuna bacin ransa kan kamawa, tsarewa da kuma gurfanar da yaran a gaban kotu
  • A cikin wata sanarwa da aka wallafa a shafukan gidan rediyon, Ahmed Musa ya bayyana lokacin da za su dawowa bakin aiki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Wani gidan radiyon kare hakkin bil'adama da ke Abuja ya dauke a wani yunkuri na nuna adawa da kamun da aka yi wa kananan yaran Arewa.

Ahmed Isah, mamallakin gidan rediyon Brekete ne ya bayyana hakan a lokacin da yake gabatar da shirin safe na gidan rediyon.

Kara karanta wannan

Matasa sun fusata, an mika bukata kan yara da gwamnatin Tinubu ta kai kotu

Ahmed Isa ya rufe gidan rediyon 'Brekete Family' kan kama kananan yaran Arewa.
An rufe gidan rediyon Brekete Family kan gurfanar da kananan yaran Arewa a kotu. Hoto: @breketeConnect, @mrfestusogun
Asali: Twitter

An katse shirin gidan rediyon Brekete

Sanarwar da gidan rediyon ya fitar a shafinsa na X ta ce Ahmed Isa wanda ya saba gabatar da shirin a ranakun aiki bai shiga dakin watsa shirin a yau ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ce wanda ake yiwa lakabi da 'ordinary president' ya ki gabatar da shirin saboda 'abin takaici' da ya faru na gurfanar da kananan yara a kotu ranar Juma'a.

An kuma ce ya kira wayar shirin da misalin karfe 8:20 na safiya, inda ya nuna bacin ransa kan tsare yaran tare da ba da umarnin a rufe gidan rediyon nan take.

Ordinary President ya fadi lokacin bude rediyon

Shugaban ya ce gidan rediyon zai ci gaba da kasancewa a rufe har zuwa ranar Talata lokacin da za a samu karin bayanai kan lamarin.

Ya ce za a sake rufe gidan rediyon har zuwa ranar Laraba, inda za a bai wa al'umma damar kira kai tsaye domin bayyana ra'ayoyinsu kan kame yaran, inji rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Lauya ya bayyana yadda aka ci mutuncin Arewa kan yaran zanga zanga

Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na ci gaba da fuskantar matsin lamba tun bayan da hotunan kananan yaran suka fara yaduwa a makon jiya.

An gurfanar da yaran Arewa a kotu

Tun fari, mun ruwaito cewa, gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta gurfanar da mutane 67 a gaban kotu kan zargin cin amanar kasa da kuma yunkurin kifar da gwamnati.

Lauyan da ya tsayawa gwamnatin Najeriya wajen shigar da karar ya karyata masu cewa kananan yara ne aka gurfanar a kotun, inda ya ce akwai masu aure a cikinsu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.