Matasa Sun Fusata, An Mika Bukata kan Yara da Gwamnatin Tinubu Ta Kai Kotu

Matasa Sun Fusata, An Mika Bukata kan Yara da Gwamnatin Tinubu Ta Kai Kotu

  • Kungiyar 'North Youth Alliance' ta kwatanta tirke kananan yara da gwamnatin Tinubu ta yi a kotu da garkuwa da mutane
  • Shugaban kungiyar, Aliyu Bin Abbas ya ce kama yara masu kananan shekaru da gurfanar da su gaban kotu ba dai-dai ba ne
  • Ya bukaci gwamnatin tarayya da ta bayar da umarnin sakin yaran tare da janye tuhumar kokarin kifar da ita da ake yi masu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna – Wata kungiyar Arewa ta ‘National Youth Alliance ta caccaki gwamnatin Bola Ahmed Tinubu game da gurfanar da kananan yara a gaban kotu.

Kungiyar, karkashin jagorancin shugabanta na kasa, Aliyu Bin Abbas ta kwatanta yadda gwamnati ta tsare yaran da tsare da garkuwa da mutane.

Kara karanta wannan

Kungiyar Arewa ta maka kafar Arewa24 a gaban kotu, dalilai sun bayyana

Gwamnati
Kungiyar Arewa ta nemi a saki yaran da aka kama a Arewa Hoto: Aliyu Bin Abbas/Baya Onanuga
Asali: Facebook

A sakon da Aliyu Bin Abbas ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya caccaki yadda gwamnati ke shari’a da yara masu karancin shekaru bisa zargin yunkurin kifar da gwamnatin Tinubu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyar Arewa ta fusata da gwamnatin Tinubu

Jaridar Punch ta wallafa cewa shugaban kungiyar NYA, Aliyu Bin Abbas ya bayyana damuwa kan yadda gwamnatin tarayya ta kama kananan yara a lokacin zanga zangar #EndBadGovernance.

Ya fadi damuwar matasan Arewa ne a wani taro da manema labarai a jihar Kaduna inda matasan shiyyar 19 su ka hallara domin jaddada matsayarsu.

“An karya dokar kare yara:” NYA

Aliyu Bin Abbas ya alakanta kamawa da gurfanar da yara masu kananan shekaru da gwamnatin Tinubu ta yi a gaban kotu a matsayin cin zarafin yara.

Ya kuma bukaci gwamnatin tarayya ta gaggauta sakin yaran, ta kuma janye tuhumar cin amanar kasa da ta ke yi masu.

Kara karanta wannan

Dattawan Arewa sun fusata kan tsare yara ƙanana, sun caccaki gwamnonin yankin

Tsohon Sanata ya fusata da shari’ar kananan yara

A baya kun ji cewa tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani ya ce gwamnatin tarayya ba ta kyauta ba a shari’ar da ta ke yi da kananan yara.

Ya shawarci Bola Ahmed Tinubu ya gaggauta bayar da umarnin sakin yaran ba tare da wani sharadi ba domin sada su da iyayensu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.