Rikicin Soja da 'Yan Sanda Ya Jawo Asarar Rayuka a Nasarawa
- Rikicin da ya ɓarke tsakanin wani jami'in soja da ƴan sanda ya yi sanadiyyar asarar rayukan mutum biyu a jihar Nasarawa
- An ce rikicin ya auku lokacin da sojan ya yi yunƙurin hana ƴan sanda tafiya da wani da ake zargin ya sace babur
- Rundunar ƴan sandan Nasarawa ta tabbatar da aukuwar lamarin wanda ya faru a ranar Lahadi, 3 ga watan Nuwamban 2024
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Nasarawa - An samu asarar rayukan mutum biyu biyo bayan ɓarkewar rikici tsakanin wani soja da wani jami'in ƴan sanda na musamman a jihar Nasarawa.
Rahotanni sun nuna cewa an samu rikicin ne a ranar Lahadi a kasuwar Agyaragu da ke ƙaramar hukumar Obi ta jihar Nasarawa.
Kakakin rudunar ƴan sandan jihar, DSP Ramhan Nansel ya tabbatar da aukuwar lamarin a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, cewar rahoton tashar Channels tv.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda soja ya yi rikici da ƴan sanda
Ya ce rikicin wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutanen ya faru ne biyo bayan wani bincike da aka gudanar kan wani rahoton satar babur, a ranar Lahadi da misalin ƙarfe 12:30 na rana.
A cewar sanarwar, bayan da aka samu labarin satar, jami’an ƴan sanda tare da haɗin gwiwar ƴan sanda na musamman da ke aiki a Jenkwe, ƙaramar hukumar Obi a kasuwar Agyaragu, sun kama wanda ake zargin.
A yayin da ake tafiya da wanda ake zargin zuwa ofishin ƴan sanda, wani soja da aka ce yana aiki a jihar Borno amma ya zo gida hutu, ya farmaki jami’an ƴan sandan da nufin hana kamen.
Sakamakon haka, sanarwar ta yi zargin cewa sojan ya fito da wuƙa ya daɓawa jami'in ƴan sanda na musamman.
"A wajen yunƙuri kare kai, an ci ƙarfin sojan sannan aka yi amfani wuƙarsa a kansa. Dukkansu sun samu raunuka daban-daban, kuma daga baya sojan da ya samu jikkata ya mutu."
- DSP Ramhan Nansel
Matasa sun ƙona ofishin ƴan sanda
Dangane da abin da ya faru, wasu matasa sun taru sannan suka afkawa ofishin ƴan sanda sannan suka ƙona shi, rahoton The Guardian ya tabbatar.
Ƴan sanda sun mayar da martani kan harin, kuma sun jikkata uku daga cikin maharan inda daga baya aka tabbatar da mutuwar ɗaya daga cikinsu.
Ƴan sanda sun daƙile harin ƴan ta'adda
A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar ƴan sandan jihar Imo ta sanar da samun nasarar ɗakile wani harin ƴan ta'adda a ranar Talata.
Rundunar ƴan sandan ta ce ta samu nasarar hallaka ɗaya daga cikin ƴan ta'addan waɗanda ake zargin na ƙungiyar IPOB/ESN ne.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng