Uwargidan Tinubu, Ribadu za Su Jagoranci Taron Addu'a kan Matsin Rayuwa
- Kusoshi a gwamnatin Bola Ahmed Tinubu za su jagoranci taron addu'a domin neman daukin Ubangiji kan matsalolin kasa
- Uwargidan shugaban kasa, Oluremi Tinubu da mashawarcinsa kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu ne za su shige gaba a taron
- Jagororin addinin musulunci da na kirista ne su ka hada taron a inuwar National Prayer Forum domin neman sauki a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Mai dakin shugaban kasa, Oluremi Tinubu da mashawarcin shugaban kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu za su jagoranci babban taron addu'a na kasa.
Za a gudanar da taron neman Allah SWT ya kawo sauki a cikin wahalhalu da sauran matsalolin da Najeriya ke ciki.
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa jagororin addinin musulunci da na kirista ne su ka shirya taron addu'o'in, ganin yadda matsala ta ki karewa a kasar nan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
NPF ta shirya addu'a kan gwamnatin Tinubu
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa kungiyar 'National Prayer Forum (NPF)' da ke yi wa kasa addu'a ta shirya taron addu'o'i ganin mawuyacin halin da jama'a ke ciki,
Darakta janar na NPF, Chief Segun Balogun Afolorunikan ya ce an yi wa taron na bana lakabin neman daukin mahalicci a kan sha'anin Najeriya.
Gwamnatin Tinubu za ta nemi daukin Mahalicci
Kungiyar 'National Prayer Forum (NPF)' ta bayyana muhimmancin aiki dare domin magance matsalolin da kasar nan ta ke fuskanta.
Chief Segun Balogun Afolorunikan ya bayyana cewa kusoshi a gwamnatin Bola Tinubu ne za su jagoranci taron addu'o'in da ake sa ran da zarar an kammala, za a samu mafita.
Gwamnatin Tinubu ta ba da shawarar samun abinci
A baya mun ruwaito cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta ba yan kasar nan hanyar da za su bi domin samun abinci da sauki yayin da ake fama da tsadar abinci da yunwa tsakanin jama'a.
Shugaba Tinubu, wanda ya yi magana ta bakin hadiminsa, Bayo Onanuga ya ce dole ne sai 'yan Najeriya sun bayar da gudunmawarsu wajen gina kasa, idan ana so a magance matsalar tsadar abinci.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng