Jihohin Arewa da Suka fi Dogaro da Kason da Gwamnatin Tarayya ke Bayarwa

Jihohin Arewa da Suka fi Dogaro da Kason da Gwamnatin Tarayya ke Bayarwa

  • Mafi yawan jihohin Najeriya na dogara ne da tallafin da Gwamnatin Tarayya ke bayarwa duk wata a kasar.
  • Jihohin Kudu a mafi yawan lokuta sune ba su cika dogara da kudin Gwamnatin Tarayya ba saboda yawan haraji da suke tarawa
  • A cikin wani rahoto da aka fitar, jihohon Lagos da Ogun sune wadanda kason dogaro da Gwamnatin Tarayya ya yi kasa sai mabi musu jihar Zamfara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Jihohi a Najeriya da dama na dogaro da kudin Gwamnatin Tarayya domin yin wasu ayyuka da biyan albashi.

Sai dai akwai jihohin da suka fi dogaro da kudin Gwamnatin Tarayyar fiye da wasu a ɓangarorin kasar.

Kara karanta wannan

Katsina: Gwamna ya fadi inda ake kyankyashe yan ta'adda cikin sauki

Gwamnonin Arewa da suka fi dogaro da kason Gwamnatin Tarayya
Akwai jihohin Arewa da dama da suka fi dogara da jiran kudin Gwamnatin Tarayya domin warware matsalolinsu. Hoto: Nigeria Governors' Forum.
Asali: Twitter

Jihohi da suka fi dogaro da Gwamnatin Tarayya

Rahoton BudgIT ya fitar da wani bincike da ke nuna jihohin da suka fi dogaro da Gwamnatin Tarayya a kan wasu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jihar Bayelsa da ke da arzikin man fetur abin mamaki tafi dogaro da kudin Gwamnatin Tarayya a kasar da kaso 92.17 sai Akwa Ibom da kaso 86.29 da kuma Delta da kaso 83.89.

Sai jihohin da suka fi karancin dogaro da kudin akwai Lagos da kaso 26.55 sai Ogun da kaso 31.95 sai kuma Zamfara da kaso 45.

Jihohin Arewa da suka fi dogaro da Gwamnatin Tarayya

1. Jihar Taraba

A cikin rahoton da aka fitar, jihar Taraba ta fi kowace jiha dogaro da kudin Gwamnatin Tarayya a Arewacin kasar da kaso 81.89.

Taraba da ke Arewa maso Gabas ta yi kaurin suna wurin arzikin noma da albarkatun kasa da ke ba da gudunmawa sosai wurin inganta tattalin arzikinta.

Kara karanta wannan

Pantami da mutane sun fusata da maka kananan yara a Kotu saboda zanga zanga

2. Jihar Niger

Niger ita ce jiha ta biyu a Arewa da tafi dogaro da kudin Gwamnatin Tarayya duk da albarkatun kasa da take takama da su.

Niger da ke Arewa maso Tsakiyar Najeriya ta dogara da kudin Gwamnatin Tarayya da kaso 80.19.

Sai dai a watan Yulin 2024, Gwamna Umaru Bago ya ce jihar ba ta dogara da kason Gwamnatin Tarayya ba, cewar Daily Post.

3. Jihar Benue

Har ila yau, Benue da ke takama da arzikin noma saboda yalwar kasa ta kasance ta uku a Arewacin Najeriya da kaso 79.85.

Jihar ita ma tana yankin Arewa ta Tsakiya da ta yi fice wurin samar da kaso mai yawa na abinci a fadin kasar baki daya.

4. Jihar Bauchi

jihar Bauchi da ke Arewa maso Gabas ta kasance ta hudu a Arewacin Najeriya da ta fi dogaro da kason da Gwamnatin Tarayya ke bata da kaso 75.33.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sake kai ƙazamin hari, sun yi garkuwa da fasinjoji sama da 20

Duba da haka jaridar Punch ta tabbatar da cewa jihohi 24 a kasar sun dogara ne kacokan da kason Gwamnatin Tarayya domin biyan albashi.

5. Jihar Nasarawa

Nasarawa ta zama ta biyar a Arewa wurin dogaro da kason Gwamnatin Tarayya da take rabawa kowane wata da kaso har 74.55, cewar The Guardian.

Ita ma jihar ta fito daga yankin Arewa ta Tsakiyar Najeriya da ke makwabtaka da jihohin Benue da kuma Plateau.

6. Jihar Gombe

Jihar Gombe ta sanu wurin gudanar da harkokin kasuwanci inda ake ganin daga jihar Kano a harkar cinikayya sai ita a Arewa, cewar BusinessDay.

Jihar da ke Arewa maso Gabashin Najeriya tana dogaro da Gwamnatin Tarayya ne da kaso 72.29.

7. Jihar Kano

Kano ta kasance ta bakwai a jerin jihohin Arewa da suka fi dogaro da kudin Gwamnatin Tarayya da kaso 70.24.

Jihar da ta yi fice fiye a Arewa game da harkokin kasuwanci ta fito ne daga Arewa maso Yammacin kasar.

Kara karanta wannan

Babu ƙabilanci a Musulunci: Sheikh Jingir ya tura sako ga Tinubu

Gwamnonin Arewa da za su biya albashin N70,000

Kun ji cewa sasu gwamnonin Arewa sun yi alkawarin fara biyan mafi ƙarancin albashi zuwa N70,000 da zarar gwamnatin tarayya ta fara.

Hakan na zuwa ne bayan Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ta fara biyan ma'aikata mafi ƙarancin albashi na N70,000 a kowane wata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.