Dattawan Arewa Sun Fusata kan Tsare Yara Ƙanana, Sun Caccaki Gwamnonin Yankin

Dattawan Arewa Sun Fusata kan Tsare Yara Ƙanana, Sun Caccaki Gwamnonin Yankin

  • Kungiyar Dattawan Arewa ta yi korafi kan yadda aka tsare yara ƙanana ba bisa ka'ida ba a birnin Tarayya Abuja
  • Dattawan sun nuna damuwa kan yadda aka tsare yaran har na tsawon watanni ba tare da musu shari'a ba
  • Hakan ya biyo bayan kame yaran a watan Agustan 2024 kan zargin shiga zanga-zangar da aka gudanar a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Kungiyar Dattawan Arewa sun yi martani kan tsare yara ƙanana na tsawon watanni a Abuja.

Dattawan sun yi Allah wadai da hakan inda suka bukaci daukar matakin gaggawa kan lamarin.

Dattawan Arewa sun yi martani kan tsare yara ba ka'ida
Dattawan Arewacin Najeriya sun nuna damuwa kan yadda aka ci zarafin yara. Hoto: Omoyele Sowore.
Asali: Twitter

Dattawan Arewa sun magantu kan tsare yara

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta fara shirin janye zarge zarge kan yara 32 a gaban kotu

Kakakin kungiyar, Abdul-azeez Sulaiman ya shaidawa The Guardian damuwarsu kan tsantsar rashin tausayi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sulaiman ya ce tsare yaran ya take hakkinsu na yan kasa kuma an saba ka'idar dokokin kasa da kasa.

Ya ce an tsare yaran na tsawon watanni uku ba tare da shari'a ba wadanda suka fuskanci bakar wahala a hannun hukumomi.

Tsare yara: Dattawan Arewa sun zargi gwamnoninsu

Daga bisani kungiyar ta zargi gwamnonin Arewa da shugabanni yankin kan kin yin wani abu game da lamarin.

"Tsarewa da kuma zargin yara mafi yawancinsu yan Arewa da cin amanar kasa wannan abin kunya ne ga kasa."
"Hakan take hakkin dan Adam a kama mutane babu dalili da kuma tsare su na tsawon lokaci babu ka'ida ya take doka."
"Sannan gurfanar da su a gaban kotu kan zarginsu da ake yi ya nuna tsan-tsan rashin bin kadunsu a matsayinsu na kananan yara."

Kara karanta wannan

Limamin masallacin Abuja, Maqary ya yi magana mai zafi sakamakon kama 'yan yara

- Cewar sanarwar Dattawan Arewa

Lauya ya koka kan tsare yara a Abuja

Kun ji cewa fitaccen lauya, Deji Adeyanju ya koka kan rashin ganin wasu daga cikin yara da aka gurfanar a gaban kotu.

Adeyanju ya yi korafin ne bayan yan sanda sun kama yaran amma lokacin gurfanar da su babu guda biyu.

Rahotanni sun ce lauyan na daga cikin masu kokarin ganin yaran sun samu adalci a zargin da ake yi musu a matsayinsu na kananan yara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.