'Yan Bindiga Sun Yi Wa Dan Majalisa Illa, Sun Hallaka Surukarsa da Dan Uwan Matarsa
- Wasu miyagun ƴan bindiga sun yi ta'asa ga iyalan ɗan majalisar wakilai da ke wakilatar Pankshin/Kanam/Kanke daga jihar Plateau
- Ƴan bindigan sun hallaka surukarsa tare da ɗan uwan matarsa a ƙaramar hukumar Jos ta Arewa a jihar Plateau
- Yusuf Adamu Gagdi ya yi alhinin wannan rashin da ya yi sannan ya yi addu'ar Allah ya tona asirin waɗanda suka aikata ɗanyen aikin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Plateau - Rahotanni sun ce wasu ƴan bindiga sun kashe wata mata mai suna Misis Mary Jonathan da ɗanta, Mark Jonathan a jihar Plateau.
Ɗan majalisar wakilai daga jihar Plateau, Yusuf Adamu Gagdi, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce waɗanda aka kashen surukarsa ce da ɗan uwan matarsa.
Ƴan bindiga sun kashe ƴan uwan ɗan majalisa
Jaridar The Nation ta rahoto cewa an kashe su ne a unguwar Mista Ali, kan hanyar Zaria a ƙaramar hukumar Jos ta Arewa ta jihar Plateau.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Har yanzu dai babu cikakkun bayanai kan yadda miyagun suka hallaka mutanen biyu.
Sai dai, an yi jana’izar mamatan guda biyu a gidansu da ke Jos babban birnin jihar Plateau a ranar Asabar, 2 ga watan Nuwamban 2024.
Ɗan majalisa ya yi alhini
Yusuf Adamu Gagdi, wanda ke wakiltar Pankshin/Kanam/Kanke, ya sanya hotuna daga wajen jana’izar a shafinsa na Facebook.
Ɗan majalisar ya bayyana kisan a matsayin tsabagen mugunta da rashin hankali. Ya kuma yi addu'ar Allah ya tona asirin waɗanda suka aikta wannan ɗanyen aikin.
"Tare da matata Jemimah, mun binne mahaifiyarta, Misis Mary Jonathan, da kuma ɗan’uwanmu, Mark Jonathan, waɗanda aka raba mu da su ta hanyar ayyukan mugunta da rashin hankali."
"Muna mutunta abubuwan tunawa da su, muna yin addu’a da neman adalci. Ku huta lafiya, Mama da ɗan uwa Mark. Allah ya a tona asirin waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aikin."
- Yusuf Adamu Gagdi
Ƴan bindiga sun kashe mutane a Benue
A wani labarin kuma, kun ji cewa rahotanni sun bayyana cewa an kashe mutane da dama a wani sabon hari da ƴan bindiga suka kai a garin Anyiin da ke ƙaramar hukumar Logo ta jihar Benue.
Ƴan bindigan sun mamaye garin ne a ranar Laraba, 30 ga watan Nuwamba da misalin ƙarfe 6:32 na yamma, inda suka kashe mutane da dama.
Asali: Legit.ng