Fitaccen Lauya Ya Bukaci Sanin Inda aka Kai Wasu Yara, Ya Ce ba a Zo da Su Kotu ba
- Wani lauya a Najeriya ta nuna damuwa kan rashin ganin sunayen yara guda biyu a cikin waɗanda aka gurfanar a kotu
- Deji Adeyanju ya ce lokacin da aka zo neman izinin kotu za a tsare su akwai sunayensu amma yanzu ba a zo da su ba
- Adeyanju ya nuna damuwa inda ya ce bai san mene ke faruwa da su ba duk da akwai bakwai wadanda ba su da lafiya a ciki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Fitaccen lauya, Deji Adeyanju ya koka kan rashin ganin wasu daga cikin yara da aka gurfanar a gaban kotu.
Adeyanju ya yi korafin ne bayan yan sanda sun kama yaran amma lokacin gurfanar da su babu guda biyu.
Lauya ya bukaci ganin yara 2 a kotu
Punch ta ce lauyan na daga cikin masu kokarin ganin yaran sun samu adalci a zargin da ake yi musu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lauyan ya ce yaran guda biyu ya kamata a gurfanar da su ne da sauran 76 a ranar Juma'a 1 ga watan Nuwambar 2024.
Adeyanju ya ce akwai sunayen yaran a takardar yan sanda lokacin da suke neman tsare su watannin baya.
"Akwai yara guda biyu da aka kama amma ba su cikin waɗanda aka kawo su kotu, ba su san mene ke faruwa ba ko wani abu ya faru da su."
"Sunayensu na cikin wadanda aka nemi tsare su amma a yanzu ba a taho da su kotu ba."
- Deji Adeyanju
Yara 7 daga ciki ba su da lafiya
Sai dai Deji ya ce akwai yara guda bakwai da ba a kawo su kotun ba saboda suna fama da rashin lafiya.
Lauyan ya ce an kai su asibitin Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja domin ba su kulawa saboda ba za su iya tsayawa a kotu ba.
SERAP ta ba Tinubu ta ba wa'adi kan yara
Kun ji cewa Ƙungiyar SERAP ta buƙaci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gaggauta umartar a saki yaran da aka tsare saboda zanga-zanga.
Ƙungiyar ta ce tsare yaran ya tauye musu haƙƙin da suke da shi na zuwa neman karatu a makaranta.
Tace za ta ɗauki matakin shari'a idan zuwa nan da sa'o'i 48 ba a saki yaran ba waɗanda ke cikin halin yunwa.
Asali: Legit.ng