Gwamnatin Tinubu Ta Fara Shirin Janye Zarge Zarge kan Yara 32 a gaban Kotu
- Akwai alamu za a iya kawo karshen zarge-zarge kan yaran da aka gurfanar da su a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke birnin Abuja
- Ministan shari'a, Lateef Fagbemi ya fara daukar matakai kan yadda za su janye zarge-zargen da ake yi kan yaran game da zanga-zanga
- Rahotanni sun tabbatar da cewa Fagbemi ya bukaci takardun shari'ar a ofishinsa domin sake duba kansu, kuma an mika su gare shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta fara shirin janye zarge-zargen da ake yi kan yaran da aka gabatar da su a gaban kotu.
Ministan Shari'a, Lateef Fagbemi shi ya fara daukar matakin kan yara 32 da aka gabatar a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.
Gwamnatin Tinubu na kokarin janye tuhuma kan yara
Punch ta ruwaito cewa awanni da gabatar da yaran a gaban kotu, Fagbemi ya nuna sha'awar shiga gaban babban sifetan yan sanda kan lamarin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Fagbemi ya tabbatar da cewa akwai abubuwa da dama da ofishinsa zai yi duba kansu kan abin da ya shafi shari'ar.
"Akwai wasu abubuwa game da shari'ar da ofishina ke son yin duba na tsanaki kansu domin daukar matakin da ya dace."
"Ba ya daga cikin iko na in saba umarnin kotu kan tsare yaran da dage shari'ar zuwa watan Janairun 2025."
"Na umarci yan sanda su kawo takardun shari'ar zuwa ofishina a jiya Asabar 2 ga watan Nuwambar 2024."
- Lateef Fagbemi, SAN
Yaushe za a sake zaman kotu?
Rahotanni sun tabbatar sifetan yan sanda ya mika takardun kuma ana kan shirin kawo karshen shari'ar cikin gaggawa.
Wata majiya ta tabbatar cewa akwai yiwuwar sake zaman kotun a farkon makon da za a shiga maimakon zuwa watan Janairun 2025.
Pantami da al'umma sun fusata kan shari'ar yara
Kun ji cewa mutane da dama sun fusata da aka ji gwamnati ta tuhumi yaran da aka kama a zanga-zanga da zargin cin amanar kasa.
Lauyan gwamnati ya fadi hikimar shigar da kara a kotun tarayya da ke Abuja, amma an soki matakin da aka dauka.
Mutane da yawa sun yi tir da yadda aka tsare kananan yaran da ke cikin yunwa, ana tuhumarsu da manyan laifuffuka.
Asali: Legit.ng