Sarkin Musulmi Ya ba Farfesa Pantami Gingimemiyar Sarauta a Daular Usmaniyya
- Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar III ya gwangwaje Farfesa Isa Ali Pantami da sarauta a daular Usmaniyya
- Sultan Muhammad Sa'ad ya ba Farfesa Pantami sarautar Majidadin Daular Usmaniyya a jiya Asabar 2 ga watan Nuwambar 2024
- Wannan ya biyo bayan gudanar da taron shekara na Sheikh Usman dan Fodiyo karo na 11 da aka saba yi a jihar Sokoto
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Sokoto - Tsohon Ministan Sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami ya samu sarautar gargajiya mai daraja a Najeriya.
Sarkin Musulmi, Sultan Sa'ad Abubakar shi ya tabbatar da Pantami a matsayin Majidadin Daular Usmaniyya.
Musabbabin ba Pantami sarauta a daular Usmaniyya
Sheikh Isa Pantami shi ya tabbatar da haka a shafinsa na X da safiyar yau Lahadi 3 ga watan Nuwambar 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sultan ya ce an ba Farfesa Pantami wannan sarauta saboda gudunmawar da yake ba masarautar tsawon shekaru 18.
Sannan daga cikin sauran abubuwan da aka duba akwai taimakon al'umma da ba da tallafi karatu ga marasa ƙarfi da kuma taimakon marayu.
Tasirin sarautar a daular Usmaniyya gaba daya
"Mai Martaba, Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III ya mika sarautar Majidadin Daular Usmaniyya ga Farfesa Isa Ali Pantami."
"Wannan sarautar ta ƙunshi dukan yankuna da shugabannin Sokoto ke jagoranta karkashin Sheikh Usman dan Fodiyo da dalibansa da aka bayar a taron shekara karo na 11."
- Farfesa Isa Ali Pantami
Sarkin Musulmi ya karawa Farfesa Isa Pantami karfin guiwar cigaba da ayyukan alheri ga al'umma kamar yadda ya saba.
Aminin Farfesa Isa Pantami mai suna Hon Muhammad Bello ya fadawa Legit Hausa farin cikinsa kan nadin sarautar.
"Ina taya Professor Isa Ali Pantami murnar samun sarautar Majidadin Daular Usmaniyya da Sultan ya karrama shi da shi, Allah ya taya shi riko kuma ya sanya albarka."
Muhammad A. Bello ya yi masa addu'a inda ya yi fatan Ubangiji ya taimake shi.
Farfesa Pantami ya ba matasan Arewa mafita
A baya, mun baku labarin cewa Farfesa Isa Ali Pantami ya bayyana cewa mutum miliyan 88.4 ke fama da matsanancin talauci kuma mafi akasari ƴan Arewa ne.
Tsohon ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani ya ce ya kamata matasa su tashi su nemi ƙwarewar fasaha da sana'o'in zamani.
Ya ce bincike ya nuna fasahar AI za ta samar da ayyukan yi miliyan 95 nan da wasu ƴan shekaru kuma za a rasa wasu ayyukan miliyan 83.
Asali: Legit.ng