Limamin Masallacin Abuja, Maqary Ya Yi Magana Mai Zafi sakamakon Kama 'Yan Yara

Limamin Masallacin Abuja, Maqary Ya Yi Magana Mai Zafi sakamakon Kama 'Yan Yara

  • Yanzu ana ta zancen Ibrahim Ahmad Maqary ne a sakamakon wasu maganganu da ya yi a babban masallacin Abuja
  • Limamin babban masallacin na kasa bai ji dadin yadda aka kai ‘yan kananan yara kotu da sunan cin amanar kasa ba
  • Farfesan ya yi alkawarin taimakawa yaran har da daukar nauyin karatun kananan da ba su zuwa makaranta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abuja - Farfesa Ibrahim Ahmad Maqary ya yi magana bayan ganin bidiyon kananan yaran da aka gurfanar a wata kotun tarayya.

Limamin babban masallaci na kasa da ke garin Abuja ya yi tir da yadda ‘dan adam yake wulakanta bayin Allah a duniyar yau.

Ibrahim Ahmad Maqary
Limamin Masallacin Abuja ya yi tir da kama kananan yara Hoto: Prof. Ibrahim Saeed Ahmad Maqary
Asali: Facebook

Ibrahim Maqary ya yi magana kan cafke yara

A wani bidiyo da wani Meeqdad Mujtaba ya wallafa a dandalin Facebook, an ji malamin ya na tir da cin zarafin kananan yara.

Kara karanta wannan

'Ban samu komai a gwamnati ba': Kanin tsohon gwamna ya kwance masa zani a kasuwa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shehin yake cewa an rufe wadannan yara na watanni, kuma aka gurfanar da su a kotu tare da yanke masu hukunci maras dadi.

Ibrahim Ahmad Maqary ya soki tun daga cafke su da aka yi lokacin zanga-zanga zuwa kotu da aka shiga har hukuncin da aka yi.

Babban limamin ya nuna cewa danyen aikin da mahukunta suka yi ya nuna kamar mutane ba su son samun rahamar Allah SWT.

Sai dai shehin ya ce sun ji labarin ana kokarin a iya shawo kan lamarin, amma ya kara da cewa hakan ba zai sa su ki cewa uffan ba.

Sheikh Ibrahim Maqary ya ce da ya yi niyyar daga wajen karatun da yake gabatarwa, ya zarce zuwa inda aka rufe ‘yan yaran.

Tsare yara ko bata sunan shugaban kasa?

Malamin ya rasa gane hikimar maka yaran da ba su san komai ba gaban kotu, yake zargin wasu ne suka shirya yin zagon-kasa.

Kara karanta wannan

Hukumar gidajen yari ta yi magana kan zargin tsare yara 72, ta fayyace gaskiya

Ganin yadda lamarin ya jawo suka a Najeriya, Sheikh Maqary ya ce watakila da gan-gan aka yi hakan domin bata shugaban kasar.

A bidiyon, limamin ya gargadi mahukanta a kan zaluntar marasa karfi a kowane addini, ya ce ba a nan ya kamata a nuna karfi ba.

Sheikh Maqary ya ja kunnen masu iko

“Idan ba haka ba a wace duniya aka taba irin wannan. Wannan bakin hukunci!
Kuma mu kullum ba mu da aiki sai karar da karfinmu a kan raunana. Raunannen fa ya na da wani mai karfi tare da shi.”

- Sheikh Ibrahim Ahmad Maqary

Tsohon malamin jami’ar ya kuma dura kan alkalan kotu da jami’an tsaro ganin yadda kotu ta yaba N10m a matsayin belin yaran.

Maqary ya jinjinawa wadanda suka tabuka abin kwarai, ya kuma shaida cewa za su dauki dawainiyar karatun masu kananan shekaru.

Ministan shari'a zai ceto 'yan yaran?

Kara karanta wannan

Bayan suka ta ko ina, gwamnatin Tinubu ta shiga lamarin yara 76 da aka kai kotu

A baya an rahoto cewa Ministan shari’a ya samu labarin an gurfanar da kananan yara a kotu saboda zanga-zanga da aka yi kwanaki.

Watakila tsoma bakin da Lateef Fagbemi SAN ya yi zai kawo karshen wahalar da yaran suka dade su na yi tun a watan Agustan 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng