Ministar Tinubu Ta Ziyarci Yaran da Aka Tsare, Ta ba Su Tallafi
- Ministar harkokin mata a gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ziyarci yaran da aka tsare saboda zanga-zanga
- Imaan Ibrahim-Sulaiman ta nuna damuwa kan yadda aka tsare yaran sakamakon tuhumar da ake yi musu
- Ta bayyana cewa tana tattaunawa da hukumomin da abin ya shafa domin ganin an kare haƙƙin yaran
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ministar harkokin mata, Imaan Sulaiman-Ibrahim, ta bayyana matuƙar damuwarta kan yadda aka tsare yara 27.
Yaran dai an gurfanar da su a kotu bayan an kama su a watan Agustan 2024, a lokacin zanga-zangar #EndBadGovernance a jihohin Kano da Kaduna.
Ministar ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Asabar, a shafinta na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ministar Tinubu ta ziyarci yara
Imaan Sulaiman Ibrahim ta kuma ziyarci inda aka tsare yaran bayan sun kasa cika sharuɗɗan belin da kotu ta ba su.
Ministar ta ce kare haƙƙin kowane yaro abu ne mafi muhimmanci, kamar yadda kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya ya tanada, da dokar kare haƙƙin yara.
Ta jaddada cewa kowane yaro, ba tare da la'akari da halin da ya tsinci kansa ba, yana da damar samun kariya, mutunci, da tsarin shari'a na adalci a ƙarƙashin doka.
Ministar ta kuma tattauna da hukumomi domin tabbatar da cewa yaran suna samun kulawar da ta dace da kuma kare haƙƙokinsu.
"Muna ci gaba da tattaunawa tare da hukumomin da abin ya shafa, da suka haɗa da ma’aikatar shari’a, ɓangaren shari’a, da cibiyoyin gyaran hali don tabbatar da cewa an hanzarta sauraron ƙarar yaran a kotunan ƙananan yara kamar yadda doka ta tanada."
- Imaan Sulaiman-Ibrahim
Gwamna Abba ya yi magana kan tsare yara
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ce gwamnatinsa za ta ɗauki dukkan matakan da suka dace domin dawo da ƙananan yara da ake kyautata zaton wasu ƴan Kano ne.
Gwamna Abba Kabir ya ce, ya umarci kwamishinan shari'a na jihar, Haruna Dederi, ya ɗauki matakin gaggawa kan lamarin.
Asali: Legit.ng