Ana Rigimar Tsare Yara 72, Jami'an Tsaro Sun Harbi Daraktan Fina Finai a Tumbi
- Daraktan daukar hoto a masana'antar Nollywood yana cikin mummunan yanayi bayan jami'an tsaro sun karbe shi a cikinsa
- Rahotanni sun tabbatar da cewa yanzu haka Don Opata yana asibiti yana karbar kulawa ta musamman a birnin Asaba
- Hakan ya biyo bayan biyo motarsu da jami'an tsaro suka yi a tunaninsu masu garkuwa ne kamar yadda suka samu rahoto
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Delta - Jami'an tsaro sun harbi wani fitaccen daraktan daukar hoto a masana'antar Nollywood.
Jami'an tsaron sun harbi matashin mai suna Don Opata da safiyar jiya Juma'a 1 ga watan Nuwambar 2024 inda yake karbar kulawa a asibiti.
Yaushe aka harbi daraktan fina-finai a Najeriya?
Leadership ta ce lamarin ya faru ne a kusa da kasuwar Mammy da ke birnin Asaba na jihar Delta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An tabbatar da cewa jami'an 'Operation Delta Hawk' ke sintiri kan zargin garkuwa da mutane inda suka taso wata mota a gaba.
A rashin sani ashe sun yi kuskure, motar masu shirya fina-finai suka biyo a tsammaninsu masu garkuwa ne.
Masu shirya fina-finan a bangarensu, sun dauka yan fashi ne sai suka yi kokarin guduwa inda jami'an tsaron suka yi harbi.
Harbin tayar motar da suka yi, ya yi sanadin samun Opata da ke jan motar a cikinsa inda aka kai shi asibiti yayin da ake yi masa aiki.
Abin da rundunar yan sanda ta ce
Rahotanni sun tabbatar da cewa a yanzu haka Opata na cikin mummunan yanayi wanda ba zai misaltu ba.
Sai dai kakakin rundunar yan sanda a jihar, SP Edafe Bright ya musanta faruwar lamarin.
Har ila yau, 'Operation Delta Hawk' ta fayyace cewa ta yi harbin ne domin tsayar da motar ba wai illata wadanda ke cikinta ba.
Jami'an tsaro sun bindige mawaki har lahira
Kun ji cewa Rundunar yan sanda da tsare wani sifetanta kan zargin hallaka wani fitaccen mawaki a jihar Enugu da ke Kudancin Najeriya.
Rundunar ta tabbatar da kama dan sandan inda ta ce an fara kaddamar da bincike kan zarginsa da kisan Okezie Mbah.
Asali: Legit.ng