Lokaci Ya Yi: Tsohon Mataimakin Gwamna a Najeriya Ya Rasu

Lokaci Ya Yi: Tsohon Mataimakin Gwamna a Najeriya Ya Rasu

  • Jihar Delta ta yi rashin ɗaya daga cikin waɗanda suka taɓa jan ragamar shugabancinta a mulkin dimokuraɗiyya
  • Tsohon mataimakin gwamnan jihar, Farfesa Amos Utuama ya yi bankwana da duniya a safiyar ranar Asabar, 2 ga watan Nuwamban 2024 a Legas
  • Marigayin wanda ya yi wa Gwamna Emmanuel Uduaghan mataimaki na tsawon shekara takwas ya kuma taɓa riƙe muƙamin kwamishinan shari'a na jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Delta - Wani tsohon mataimakin gwamnan jihar Delta, Farfesa Amos Utuama, ya rasu.

Marigayin wanda babban lauyan Najeriya (SAN) ne, ya rasu da sanyin safiyar ranar Asabar, 2 ga watan Nuwamban 2024 a Legas.

Tsohon mataimakin gwamnan Delta ya rasu
Farfesa Amos Utuama ya rasu a Legas Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jaridar Tribune ta rahoto cewa an haifi Amos Utuama a ranar 5 ga watan Yuni, 1947.

Kara karanta wannan

Kwana ya ƙare: Tsohon mataimakin shugaban majalisa ya rasu a hatsari

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon mataimakin gwamnan Delta ya rasu

Marigayin ya kasance mataimakin tsohon Gwamna Emmanuel Uduaghan, kuma dukkansu sun yi shekara takwas a jam'iyyar PDP, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.

Sai dai, ya kasance kwamishinan shari’a kuma Antoni Janar na jihar Delta a ƙarƙashin gwamnatin tsohon Gwamna James Ibori.

Har yanzu dai Iyalan marigayin ba su sanar da rasuwarsa a hukumance ba.

Kafin shigarsa siyasa, Farfesa Utuama ya kasance babban malami a tsangayar shari'a ta jami'ar Legas.

Marigayin ɗan asalin garin Otughievwen (Otu-Jeremi) ne a masarautar Ughievwen ta ƙaramar hukumar Ughelli ta Kudu a jihar Delta.

Tsohon mataimakin gwamnan y koma baya jin daɗin rayuwa tun bayan rasuwar matarsa Dokta Nelly Utuama, kuma ya sha kwanciya a asibiti.

Karanta wasu labaran kan rashe-rashe

Kara karanta wannan

Gwamna Uba Sani ya amince da sabon mafi karancin albashi ga ma'aikatan Kaduna

Tsohon minista ya rasu

A wani labarin kuma, kun ji cewa an shiga jimami bayan rasuwar tsohon minista kuma tsohon shugaban Arewa Consultative Forum (ACF), Cif Gabriel Aduku.

Cif Gabriel Aduku ya rasu ne a ranar Litinin 11 ga watan Maris 2024 a ƙasar Amurka bayan ya sha fama da jinya mai tsayi.

Marigayin kafin rasuwarsa ya rike karamin ministan lafiya a Najeriya kafin daga bisani ya bar kujerar kungiyar ACF.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng