'Rashin Tausayi ne': Sanata a Arewa Ta Yi Allah Wadai da Kai Yara Kotu, Ta Nemo Mafita
- Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da ke wakiltar Kogi ta Tsakiya ta yi Allah wadai da tsare ƙananan yara ba bisa ka'ida ba
- Sanata Natasha ta ce akwai tsantsar rashin tausayi da adalci a tsare yara ƙanana ba tare da kulawa ta abinci ba
- Wannan na zuwa ne bayan tsare wasu yara na tsawon watanni kan zargin shiga zanga-zangar adawa da gwamnatin Bola Tinubu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kogi - Yayin da ake cigaba da korafi kan tsare kananan yara a Abuja, Sanata daga Arewa ta yi Allah wadai kan abin da ke faruwa.
Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da ke wakiltar Kogi ta Tsakiya ta ce abin da ya faru tsantsar rashin adalci ne da tausayi.
Zanga-zanga: Sanata ya bukaci bincike game da yara
Sanatar ta fadi haka ne ta bakin sakataren yada labaranta, Arogbonlo Israel a yau Asabar 2 ga watan Nuwambar 2024, cewar Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanata Natasha ta bukaci shugabar alkalan Najeriya, Kudirat Kekere-Ekun ta yi bincike kan lamarin domin hukunta masu hannu a cin zarafin yaran.
Ta ce akwai rashin tausayi da imani a tsare yara ƙanana ba tare da isasshen abinci da ba su kulawa na musamman ba.
Sanata ta ba shugaban gidajen yari shawara
Sanata Natasha ta ce an take musu hakki inda ta ce ya kamata a gurfanar da su ne a kotun laifuffuka na ƙananan yara ba tare da bayyana fuskokinsu ba.
Har ila yau, Natasha ya bukaci shugaban gidajen yari, Haliru Nababa ya binciki gidan yarin Kuje da yanayinsa duba da rashin kulawa mai inganci a wurin.
Abba ya magantu kan yaran da aka kama
Kun ji cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi magana kan yaran da aka gurfanar a gaban kotu saboda zanga-zanga.
Gwamna Abba ya bayyana cewa ya umarci kwamishinan shari'a na jihar ya ɗauki matakin gaggawa kan lamarin.
Gwamnan ya ba da tabbbacin cewa za su.yi duk mai yiwuwa domin ganin yaran sun dawo zuwa jihar Kano nan da lokaci kankani.
Asali: Legit.ng