Rai Ya Yi Halinsa: Shugaban Karamar Hukuma Ya Yi Mutuwar Bazata, an Samu Bayanai
- Al'ummar karamar hukumar Onigbongbo a jihar Lagos sun shiga jimami bayan rasuwar shugabansu a yau Asabar
- Marigayin mai suna Oladotun Olakanle ya rasu ne da safiyar yau Asabar 2 ga watan Nuwambar 2024 a jihar
- Rahotanni sun tabbatar da cewa wannan shi ne karo na biyu da shugaban karamar hukumar Onigbongbo ke rasuwa a kan mulki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Lagos - An shiga rudani a jihar Lagos bayan mutuwar bazata da shugaban karamar hukuma ya yi cikin wani irin yanayi.
Hakan ya faru ne bayan rasuwar shugaban karamar hukumar Onigbongbo, Oladotun Olakanle a yau Asabar 2 ga watan Nuwambar 2024.
Lagos: Yaushe shugaban karamar hukumar ya rasu?
Vanguard ta ce marigayin ya rasu ne da safiyar yau Asabar 2 ga watan Nuwambar 2024 yana da shekaru 54 a duniya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai har zuwa lokacin tattara wannan rahoto ba a tabbatar da silar mutuwar dan siyasar ba da hargitsa al'ummar yankinsa a jihar.
Rahotanni sun tabbatar cewa marigayin ya halarci bikin binne jigon APC, Dakta Adesola Taiwo a ranar 31 ga watan Oktoban 2024.
Har ila yau, a jiya Juma'a 1 ga watan Nuwambar 2024 ya raba motoci ga rundunar yan sanda a karamar hukumar domin dakile matsalar tsaro.
Yadda tarihi ya maimaita kansa a karamar hukumar
Wannan shi ne karo na biyu da shugaban karamar hukumar Onigbongbo mai ci ke mutuwa a wa'adinsu na biyu a jihar Lagos.
Kaifin rasuwar Oladotun Olakanle, wanda ya sauka ya ba shi kujerar, Babatunde Oke shi ma ya rasu a wa'adinsa na biyu sanadin annobar Covid-19, cewar rahoton PM News.
Kwara: Tsohon dan Majalisar Tarayya ya rasu
Kun ji cewa ana jimamin rasuwar tsohon shugaban hukumar zabe, an sake rashin tsohon dan Majalisar Tarayya daga jihar Kwara.
Marigayin, Hon. Aliyu Ahman- Pategi shi ne ya wakilci mazabar Edu/ Patigi a jihar Kwara na tsawon shekaru 12.
An tabbatar da cewa marigayin ya rasu ne a ranar Alhamis 24 ga watan Oktoban 2024 yana da shekaru 59 a duniya.
Asali: Legit.ng