'Ƴan Sanda Sun Samu Gagarumar Nasara kan Masu Garkuwa da Mutane
- Rundunar ƴan sandan Najeriya reshen jihar Bauchi ta samu nasarar rage mugun iri na wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne
- Kwamishinan ƴan sandan jihar ya bayyana cewa jami'an rundunar sun samu nasarar hallaka masu garkuwa da mutane mutum shida a ƙaramar kumar Ningi
- Auwal Musa ya kuma sanar da cewa sun yi nasarar ƙwato makamai tare da daƙile ayyukan ta'addanci a wasu ƙananan hukumomin jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Bauchi - Rundunar ƴan sandan Bauchi ta ce jami’anta sun samu nasara kan masu garkuwa da mutane a jihar.
Rundunar ƴan sandan ta ce jami'anta sun kashe wasu mutane shida da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a wani samame da suka kai a ƙaramar hukumar Ningi da ke jihar.
Kwamishinan ƴan sandan jihar, Auwal Musa, ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Juma'a, cewar rahoton jaridar TheCable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan sanda sun kashe masu garkuwa da mutane
Kwamishinan ya sandan ya kuma bayyana cewa jami'an rundunar sun samu nasarar ƙwato makamai da alburusai, rahoton jaridar The Nation ya tabbatar.
"Ba kawai mun ƙwace makamai da alburusai daga hannun mutane ba, mun kuma daƙile ayyukan ta’addanci a yankunan ƙananan hukumomin Alkaleri, Ningi, da Toro na jihar Bauchi.”
"Jami’an rundunar da ke yankin Ningi sun fafata da wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a ƙauyukan Balma, Dogon Ruwa, Lumbu, da tsaunin Burra, duk a cikin ƙaramar hukumar Ningi."
"A yayin arangamar, ƴan sanda sun kashe ƴan bindiga shida, yayin da wasu da dama suka arce zuwa cikin daji, mai yiwuwa ɗauke da harbin bindiga."
Auwal Musa
Kwamishinan ya ce rundunar na haɗa kai da sauran hukumomin tsaro da masu ruwa da tsako domin kare rayuka da dukiyoyin mutane.
Ƴan sanda sun daƙile harin ƴan ta'adda
A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar ƴan sandan jihar Imo ta sanar da samun nasarar ɗakile wani harin ƴan ta'adda a ranar Talata, 29 ga watan Oktoban 2024.
Rundunar ƴan sandan ta ce ta samu nasarar hallaka ɗaya daga cikin ƴan ta'addan waɗanda ake zargin na ƙungiyar IPOB/ESN ne.
Asali: Legit.ng