Hisbah Ta Titsiye Dattijon Nan Kan Zafafan Hotunan da Ya Wallafa Tare da Ƴan Mata
- Hisbah ta kama Bala Muhammed, mutumin nan da ake ta surutu kan hotunan da ya wallafa shi da ƴan mata daban-daban a Bauchi
- Hukumar ta Bauchi ta masa tambayoyi a ofishinta sannan ta maida shi hannun ƴan sanda domin ci gaba bincike
- Bala Muhammed ya yi bayani kan yadda aka ɗauki hotunan tare da bai wa iyalan ƴan matan hakuri kan abin da ya aikata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Bauchi - Rundunar ƴan sandan Musulunci watau Hisbah ta jihar Bauchi ta kama mutumin nan ɗan shekara 76 a duniya, Bala Muhammad da ake kira Bala Marke.
Dakarun Hisbah sun titsiye dattijon da tambayoyi a ofishinsu kan hotunan da ke yawo a soshiyal midiya, wanda aka ganshi tare da mata daban-daban.
A ƴan kwanakin nan dai babu abin da ke yawo kuma ya ɗauki hankalin jama'a musamman ƴan Arewa a kafafen sada zumunta kamar hotunan Bala Marke.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda hotunan Bala suka ɗauki hankali
Daily Trust ta tattaro cewa Bala ya wallafa hotuna da ƴan mata kusan guda 30, galibin matan sun nuna wasu sashi na jikinsu.
Yawancin ƴan matan da Bala ya ɗauki hotunan da sua suna da matsakaicin shekaru kuma sun yi kwalliya mai ɗaukar hankali.
Hotunan sun haifar da ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta, inda wasu suka ba mazan Bauchi masu mata shawarin su yi taka tsantsan da Bala Muhammad.
Hisbah ta yiwa mutumin tambayoyi
A wani taron manema labarai, mukaddashin kwamandan Hisbah a Bauchi, Muhammad Bununu, ya ce samu korafe-korafe daga iyalan matan da ke cikin hotunan.
Ya ce rundunar ƴan sanda ta kama mutumin amma duk da haka suka nemi a ba su shi domin ya amsa tambayoyi.
"Da farko ƴan sanda suka cafke shi, amma muka nemi a kawo mana shi domin ya amsa tambayoyi. Bayan mun gama bincikenmu ranar Alhamis, muka mayar da shi hannun ƴan sanda."
Bala Muhammed ya ba da haƙuri
A wani faifan bidiyon hirarsa da Hisbah, Bala ya yi bayanin cewa an dauki hotunan kimanin shekaru ashirin da suka gabata lokacin akasarin matan ba su yi aure ba.
Ya kuma bai wa iyalai da matan hakuri kan duk wata damuwa da matsalar da wallafa hotunan ya jawo masu.
Hisbah za ta shiga cikin ma'aikata a Kano
A wani rahoton, an ji cewa majalisar dokokin Kano ta yaba da ayyukan ƴan Hisbah, ta fara kokarin ƙara masu albashi da alawus-alawus duk wata.
Ɗan majalisa mai wakiltar Minjibir, Abdulhamid Abdul ya gabatar da kudirin da ya nemi a maida ƴan Hisbah cikin ma'aikatan gwamnati.
Asali: Legit.ng