Kwankwaso Ya Soki Gurfanar da Kananan Yara a Kotu, Ya ba Gwamnati Shawara

Kwankwaso Ya Soki Gurfanar da Kananan Yara a Kotu, Ya ba Gwamnati Shawara

  • Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya yi magana kan gurfanar da ƙananan yara a gaban kotu da rundunar ƴan sanda ta yi
  • Kwankwaso ya soki matakin kan yaran a gaban kotu inda ya ce kamata ya yi a.ce yana suna makaranta
  • Ya buƙaci hukumomin da abin ya shafa ɗa su gaggauta duba tuhume-tuhumen domin yaran su koma.ga iyalansu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi'u Kwankwaso, ya yi Allah-wadai da gurfanar da ƙananan yara 67 da rundunar ƴan sanda ta yi a Abuja bisa zarginsu da gudanar da zanga-zangar #EndBadGovernance.

Da yake bayyana kaɗuwarsa da faruwar lamarin, Kwankwaso ya nuna matuƙar damuwarsa kan abinda aka yi wa yaran.

Kara karanta wannan

Muguntar T pain: Atiku ya caccaki gwamnatin Tinubu kan kai yara kotu

Kwankwaso ya yi magana kan kai yara kotu
Kwankwaso ya soki gurfanar da yara a kotu saboda zanga-zanga Hoto: @KwankwasoRM, @YeleSowore
Asali: Twitter

Kwankwaso ya soki matakin ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X a ranar Juma'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwankwaso ya soki kai yara kotu

Kwankwaso ya bayyana cewa halin da suke ciki ya nuna suna cikin rashin samun abinci mai gina jiki kuma suna buƙatar kulawar gaggawa.

"Waɗannan yara, waɗanda a fili suke cikin halin yunwa da buƙatar samun kulawar likita, sun fuskanci mummunan yanayi lokacin da ya kamata su kasance a makaranta."
"Gurfanar da waɗannan yaran masu yawa a halin da suke ciki, abu ne da ba a saba ganin irinsa ba, kuma ya saɓa duk wata ƙa’ida ta ƴancin ɗan Adam da mutunci."
"A matsayinmu na shugabanni, haƙƙinmu ne mu kare waɗanda suka fi kowa rauni a cikinmu, musamman yara, mata, tsofaffi, da mabuƙata. Bai kamata gwamnati ta kasance a sahun gaba wajen wannan cin zarafi ba."

Kara karanta wannan

Kaico: Wani matashin yaro ɗan shekara 16 ya hallaka kishiyar mahaifiyarsa

"Wauta ce a buƙaci yaro ya nemo Naira miliyan 10 da ma’aikaci mai mataki na 15 a matsayin wanda zai tsaya masa ya samu beli."
"Ina roƙon hukumomin da abin ya shafa da su sake duba waɗannan tuhume-tuhume cikin gaggawa domin yaran su koma ga iyalansu."

- Rabiu Musa Kwankwaso

Atiku ya caccaki kai ƙananan yara kotu

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya yi magana kan ƙananan yaran da aka tsare tare da gurfanar da su gaban kuliya kan zanga-zangar #EndBadGovernance.

Atiku Abubakar ya caccaki gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin shugaba Bola Tinubu kan tsare ƙananan yaran tare da gurfanar da su gaban kuliya saboda zanga-zanga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng