Rashin Lantarki: An Fara Haɗa Alkaluman Asarar Arewa, Za a Nemi Diyya daga Tinubu
- Gidauniyar Jino da ke rajin kare hakkin dan Adam a Arewacin kasar nan ta ce akwai bukatar gwamnati ta biya mazauna yankin diyya
- Shugaban kungiyar kuma tsohon dan takarar gwamna a Katsina, Imran Jafaru Jino ya ce sun fara yunkurin tattara alkaluma
- Ya ce za a tattara bayanan ta kafar intanet, sannan jami'an da za su dauka za su bi mutanen da ba su da ilimin na'ura mai kwakwalwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Katsina - Tsohon dan takarar gwamna a Katsina kuma shugaban gidauniyar Jino, Imran Jafaru Jino zai jagoranci neman diyyar asara da yan Arewa su ka tafka saboda rashin wuta.
Alkaluman da kungiyoyin a shiyyar su ka fitar ya nuna cewa jama'a sun yi asarar sama da N1.5trn bayan rashin wuta daga 9 Satumba zuwa 30 Satumba.
A zantawarsa da Legit, shugaban gidauniyar Jino, Imran Jafaru Jino ya ce sun fitar da hanyoyin tattara bayanan wadanda su ka yi asara saboda rashin hasken lantarkin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lantarki: Za a tattara bayanan yan Arewa
BBC ta ruwaito tsohon dan takarar gwamna a shekarar 2023 karkashin jam'iyyar PRP, Imran Jafaru Jino ya ce za su samar da manhajar tattara bayanan yan Arewa.
Ya ce za a iya fitar da bayanan da mutum zai cike a kafar intanet domin su samu bayanan da ake bukata, sannan za a fitar da hanyar bibiyar sahihancin bayanan.
Arewa: Gidauniya ta fusata da rashin lantarki
Jino ya kara da cewa sun yi mamakin yadda ba su ji komai kan batun ragewa jama'ar Arewa wani abu na asara da su ka tafka ba.
Ya ce rashin lantarkin da har yanzu bai daidaita ba ya jawo matsaloli ga masu sayar da kajin da ake shigo da su daga ketare, mata masu sana'a a cikin gida da sauran manyan kasuwanci.
IHRC ta ce an take hakkin Arewa
A baya mun ruwaito cewa hukumar kare hakkin dan Adam ta 'International human rights commission (IHRC) ta ce jimawa da Arewa ta yi babu lantarki tauye hakki ne.
Shugaban hukumar reshen Najeriya, Ambasada Abdullahi Bakoji ne ya bayyana haka, inda ya tabbatar da cewa mazauna yankin sun tafka asarar abin da ya haura N1.5trn.
Asali: Legit.ng