Jami'an EFCC Sun Kama Akanta Janar da Wasu Hadiman Gwamna 4, Bayanai Sun Fito
- EFCC ta kama Akanta Janar na jihar Edo, Julius O. Anelu da wasu jami'ai hudu da ke da alhakin fitar da kudi daga asusun gwamnati
- Rahotanni sun nuna cewa EFCC ta kama mutanen ne domin hana fitar da kudi yayin da wa'adin Gwamna Obaseki ke dab da karewa
- Wannan mataki na zuwa ne kwanaki 11 gabanin Obaseki ya miƙa mulki ga zababben gwamna, Monday Okpebholo
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Edo - Hukumar yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'adi watau EFCC ta cafke Akanta Janar na jihar Edo, Mr. Julius O. Anelu da wasu manyan jami'ai huɗu.
Wannan kame na zuwa ne kwanaki 11 gabanin Gwamna Godwin Obaseki mai barin gado ya miƙa mulki ga zaɓaɓɓen gwamna, Monday Okpebholo na APC.
Daily Trust ta tattaro cewa an cafke waɗannan ƙusoshin gwamnatin Obaseki ne ranar Alhamis kuma yanzu haka suna tsare a ofishin hukumar EFCC na Benin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin EFCC na kama Akanta Janar
Wasu bayanai sun nuna cewa EFCC ta tsare jami'an ne domin hana cire kuɗi daga lalitar gwamnatin Edo biyo bayan wani kasafi da ake zargin majalisar dokoki ta amince.
Wata majiya ta ce kama Akanta Janar da sauran mutane huɗu ya dakatar da dukkan ayyukan gwamnati saboda su kaɗai ke iya sa hannu wajen cire kudi a baitul-mali.
A cewar majiyar, lamarin ya kawo cikas a harkokin gwamnatin Edo domin a yanzu ba ta iya biyan alawus-alawus na ma'aikata, ƴan fansho da sauransu.
EFCC za ta sake su bayan rantsar da gwamna
Ta ƙara da cewa EFCC ta kudiri aniyar ci gaba da tsare jami’an da aka kama har zuwa ranar 12 ga watan Nuwamba, lokacin da wa’adin gwamnatin mai barin gado zai kare.
Da aka tuntubi kakakin EFCC na jihar Edo, Williams Oseghale, ya umarci manema labarai su nemi mai magana da yawun hukumar na ƙasa, Dele Oyewale.
Da aka tuntube shi ta wayar tarho, Oyewale ya bukaci a aiko da sakon tes amma har yanzum bai dawo da amsa ba.
EFCC ta gurfanar da tsohon gwamnan Kwara
A wani rahoton, an ji cewa hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya ta sake gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kwara a gaban kotu.
EFCC ta shigar da sababbin tuhume-tuhume a kan Abdulfatah Ahmed da kwamishinansa na kuɗi kan zargin karkatar da N5.78bn.
Asali: Legit.ng