Bayan Suka Ta Ko Ina, Gwamnatin Tinubu Ta Shiga Lamarin Yara 76 da Aka Kai Kotu
- Ministan shari’a a Najeriya ya samu labarin gurfanar da kananan yara da aka yi saboda sun fito zanga-zanga kwanaki
- Lateef Fagbemi SAN ya umarci ‘yan sanda su damka masa takardun shari’ar domin a iya kawo karshen wannan shari’a
- Ofisishin lauyan gwamnatin tarayya zai duba halin da ake ciki bayan mutane daga gida da waje sun soki tsare yaran
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya, ya yi maganar gurfanar da kananan yara da aka yi a kotu.
Lateef Fagbemi SAN ya tsoma baki a lamarin ne bayan kungiyoyi da mutane dabam-dabam sun yi ca a kan gwamnatin tarayya.
Za a karbi shari'ar yara masu zanga-zanga
Rahoton da The Cable ta fitar dazu da dare ya bayyana cewa Lateef Fagbemi ya bukaci ‘yan sanda su mika masa takardun karar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yara akalla 76 aka shigar da kararsu a kotu bisa zargin laifuffukan da suka da cin amanar kasa da neman hambarar da gwamnati.
A wani jawabi da ya fitar ranar Juma’a, Ministan shari’a ya bayyana cewa zai duba lamarin domin daukar matakin da ya kamata.
Minista ya samu labarin shari'a da yara
"Labari ya zo gare ni cewa ‘yan sanda sun gurfanar da wadanda ake zargi da hannu a mummunan zanga-zangar #EndBadGovernance a kotu saboda laifuffuka iri-iri daga ciki har da cin amanar kasa.
"Wadannan su na cikin batutuwan da ofishina yake bukatar ya duba domin ya iya daukar matakin da ya kamata.
- Lateef Fagbemi SAN
Watakila gwamnati ta nemawa yaran sauki
Daily Nigerian ta rahoto shi ya na mai cewa ya san alkali ya yi umarni a cigaba da garkame wadanda ake kara zuwa Junairu.
Ministan ya ce bai da hurumin soke hukuncin da aka yanke na tsare su a gidan maza ko kuma daga shari’ar da aka yi zuwa badi.
Saboda haka ya umarci rundunar ‘yan sanda ta sallama masa takardun shari’ar, za a yi wannan ne a yau Asabar 2 ga Nuwamba.
Bayan nan, lauyan ya nemi a canza lokacin da ya kamata kotun tarayyar ta sake yin zama da nufin a shawo kan lamarin da wuri.
Gurfanar da yara a kotu ya bata gwamnati
Ana da labari cewa mutane musamman daga Arewa sun caccaki gwamnatin Bola Tinubu da jami'an tsaro game da tsare ‘yan yara.
Farfesa Isa Ali Pantami wanda tsohon Minista ne bai ji dadin hukuma ta cafke kananan yaran da ake tsoron tuni yunwa ya ci su ba.
Asali: Legit.ng