Jamnaga, Dangote da Jerin Manyan Matatun Mai 10 da Suka Fi Girma a Fadin Duniya
Abuja - Idan an hako danyen mai, ana tace su ne a matatu wadanda suke samar da abubuwan da ake bukata na rayuwa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
A wadannan matatu ne ake fitar da da fetur, kananzir, dizil, CNG da dai sauransu wadanda ake amfani da su a matsayin makamashi.
Rahotanni sun kawo jerin manyan matatun man da suka fi girma a duniya.
Matatun da suka fi girma a duniya
1. Matatar Jamnagar
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahoton The Nation ya tabbatar da cewa matatar nan ta Jamnagar da ke kasar Indiya ta fi kowace girma a yau a duk duniya.
Wannan matata da ke Jamnagar a garin Gujarat, India ta na iya tace gangunan danyen mai miliyan 1.24 a kowace ranar Allah.
2. Matatar Paraguana
Wata babbar matata da ake ji da ita yau, ita ce Paraguana da ke kasar Venezuela wanda ta yi fice da arzikin mai a nahiyar Amurka.
Wanda ya mallaki wannan matata mai iya tace ganguna 940, 000 a rana shi ne Petróleos de Venezuela wanda yake Paraguaná.
3. SK Energy Ulsan
Akwai matatar SK Energy Ulsan Complex a kasar Koriya ta Kudu, ta na cikin manyan matatun danyen mai mafi girma, an gina ta ne a 1964.
Kamfanin SK Energy ya mallaki matatar da ke yankin Ulsan a kasar Asiyar. A kowace rana ana cewa za ta iya tace ganguna 900. 000.
4. Matatar Ruwais
A hadaddiyar daular Larabawa watau UAE, akwai matatar Ruwais wanda a duk rana ta na da ikon tace gaunguna akalla 827, 000.
Wannan matata ta na nan a Ruwais a yammacin kasar UAE. Kamfanin Abu Dhabi National Oil Company (ADNOC) ya mallake ta.
5. Matatar Yeosu
Har ila yau a kasar Koriya ta Kudun akwai wata katuwar matata da ke da ikon tace ganguna fiye da 800, 000 a kowace rana.
Ba kowa ba ne ya mallaki wannan matata da ke yankin Yeosu a kasar ta Koriya sai GS Caltex kamar yadda rahoto ya tabbatar.
6. Matatar Onsan
Matata ta uku kuma ta karshe daga Koriya ta Kudu a jerin nan ita ce ta Onsan wanda ta ke iya tace ganguna 669, 000 a kullum.
Kamfanin S-Oil Corporation ya ke rike da matatar da ke lardin Onsan a Koriya. An gina matatar nan ne tun a cikin shekarar 1976.
7. Matatar Dangote
Idan aka zo Afrika, babu wata matata da ke da girma kamar ta kamfanin Dangote wanda mai kudin nahiyar ya gina ta a jihar Legas.
Jaridar Business Day ta ce matatar na da karfin tace ganguna 650, 000. Wannan zai ba da damar samun litocin fetur miliyan 50 kullum.
8. Matatar Galveston Bay
A wani jeri da Daily Trust ta fitar kwanaki, ta kawo matatar Galveston Bay a cikin wadanda a yanzu sun fi kowane girma a duk duniya.
Matatar Galveston Bay ta na nan a birnin Texas da ke kusa da Mexico a kasar Amurka. A kullum ana iya tace ganguna 631, 000.
9. Matatar Beaumont
Wata matatar mai da ke Amurka da ke cikin mafi girma ita ce ta Beaumont wanda babban kamfanin nan na Exxon Mobil ya mallaka.
Kamar dai takwararta watau Galveston Bay, matatar nan da ke makwabtaka da ita za ta iya tace gangunan danyen mai 630, 000 a yau.
10. Matatar Port Arthur
Matatar da aka rufe sahun goman farko da ita ba kowace ba ce illa Port Arthur wanda ita ma dai tana nan a Port Arhut a Texas.
Matatar ta na cikin manyan matatun Amurka wanda ta ke iya tace ganguna 600, 000 a kowace rana, ta yi suna sosai a duk duniya.
Matatar Dangote za ta samu daga Ghana
Ghana ta nuna sha'awarta kan matatar Dangote, rahoto ya zo cewa kasar Afrikan ta shirya yi mata ciniki bayan kaddamar da ita.
Wannan na zuwa ne lokacin da ake jan kafa kan sayar da fetur din a kasar nan saboda sabani da mahukunta da 'yan kasuwa.
Asali: Legit.ng