Pantami da Mutane Sun Fusata da Maka Kananan Yara a Kotu saboda Zanga Zanga
- An yi matukar mamaki da aka ji gwamnati ta tuhumi yaran da aka kama a zanga-zanga da zargin cin amanar kasa
- Lauyan gwamnati ya fadi hikimar shigar da kara a kotun tarayya da ke Abuja, amma an soki matakin da aka dauka
- Mutane da yawa sun yi tir da yadda aka tsare kananan yaran da ke cikin yunwa, ana tuhumarsu da manyan laifuffuka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Jama’a sun yi ca a kan gwamnatin tarayya da Bola Ahmed Tinubu ya ke jagoranta saboda shari’a da kananan yara.
Gwamnatin Najeriya ta gurfanar da yara da ake zargi masu kananan shekaru ne da zargin neman hambarar da farar hula.
Legit Hausa ta bibiyi yadda mutane musamman a dandalin sada zumunta su ka yi tir da matakin da gwamnati ta dauka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mutane sun ji haushin shari'a da yara
Abin da ya fusata su shi ne ganin yadda aka tsare wadannan yara na fiye da kwanaki uku saboda sun fita zanga-zanga tun Agusta.
Haka zalika ana zargin cewa ba su kai shekara 18 ba balle a gurfanar da su gaban kotu wanda ya jawo suka daga Atiku Abubakar.
Bayan nan ana tuhumar jami’an tsaro da rashin kula da su da kyau duba da yanayin da aka ga mafi yawansu a cikin kotu.
Bugu da kari sai aka ga alkali ya yaba Naira miliyan 10 a matsayin belinsu bayan tafiya da aka yi da su zuwa birnin Abuja.
Pantami ya yi tir da kama kananan yara
A shafinsa na X, Isa Ali Pantami ya yi kira ga ‘yan sanda su yi maza su dauki mataki kare wadannan bayin Allah da ya gani.
Tsohon ministan ya yi tir bayan ganin bidiyon yaran a kotu, yake cewa bai kamata sake bari irin haka ta kuma faruwa ba.
Adeyanju Deji ya koka a shafin Facebook, yake cewa an wuce da yaran zuwa gidan yari da ke Kuje saboda sun gaza samun beli.
Dan gwagwarmayan da yanzu ya zama lauya ya ce sai da ya yi kuka ranar Juma’a a kotu ganin cewa da wahala a saki yaran.
Wani Dr. Abubakar Hidima ya zargi gwamnati da tsare wadannan yara babu gaira babu dalili, ya kuma bukaci a fito da su.
An zargi alkalai da 'yan sanda da zalunci
Jafar Jafar wanda fitaccen ‘dan jarida ne ya yi Allah wadai da alkali da ‘yan sanda, ya ce da hannunsu a duk wani zalunci a kasar.
“Babu azzalumai a ƙasar nan da su ka wuce gurɓatattun alƙalai da ‘yansanda. Duk wani zalunci da ɗan siyasa zai yi a ƙasar nan sai da sahalewar su.
Allah Ka fitar da wadannan yara daga wannan ƙangi.”
- Jafar Jafar
Amnesty ta tsayawa yaran da aka kama
Dama can BBC Hausa ta rahoto cewa kungiyar kare haƙƙin bil-adama ta Amnesty a Najeriya ta yi tir da gurfanar da yaran.
Amnesty Intl ta ce kama mutanen ya saɓa wa dokokin kare haƙƙi na ƙasa da ƙasa.
Peter Obi ya nemi a binciki tsare yaran
Ana haka kuma aka ji Peter Obi ya bukaci ministan shari'a da jami’an tsaro su yi bincike kan yadda aka gallazawa kananan yaran.
‘Dan takaran shugaban kasar na LP a 2023 ya yi magana a X, yake cewa bidiyon kananan yaran a gaban alkali abin tada hankali ne.
Dalilin gurfanar da kananan yara a kotu
Dazu aka ji cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta ce yaran da aka gani a kotun tarayya duk sun haura shekara 18 da haihuwa.
Lauyan gwamnati watau Barista Rimazonte Ezekiel ya ce a cikin wadanda aka kama akwai masu iyali da wadanda sun gama jami’a.
Asali: Legit.ng