Muguntar T Pain: Atiku Ya Caccaki Gwamnatin Tinubu kan Kai Yara Kotu

Muguntar T Pain: Atiku Ya Caccaki Gwamnatin Tinubu kan Kai Yara Kotu

  • Atiku Abubakar ya yi Allah wadai da matakin gwamnatin tarayya na gurfanar da ƙananan yara gaban kotu saboda zanga-zanga
  • Tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya caccaki matakin inda ya bayyana cewa rashin tausayi ne a gurfanar da kananan yara
  • Atiku ya nuna cewa abin takaici ne yadda aka gurfanar da yaran a kotu saboda sun yi adawa da wasu manufofin gwamnati

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishai

FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya yi magana kan ƙananan yaran da aka tsare tare da gurfanar da su gaban kuliya kan zanga-zangar #EndBadGovernance.

Atiku Abubakar ya caccaki gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin shugaba Bola Tinubu kan tsare ƙananan yaran tare da gurfanar da su gaban kuliya saboda zanga-zanga.

Kara karanta wannan

"Ana abin kunya:" Tsohon sanata ya ba Tinubu shawara kan shari'a da kananan yara

Atiku ya caccaki gwamnatin Tinubu
Atiku ya soki gurfanar da yara gaban kotu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Atiku ya bayyana hakan ne a cikin wani rubutu da ya yi a shafinsa na X a ranar Juma'a, 1 ga watan Nuwamban 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani faifan bidiyo mai tayar da hankali ya nuna yadda yaran waɗanda duk sun galabaita an gurfanar da su a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja.

Atiku ya caccaki gwamnatin Tinubu

A cewar Atiku, gurfanar da waɗannan yaran da ake zargi da hannu a zanga-zangar da ta faru tsakanin 1 ga watan Agusta zuwa 10 ga Agusta, 2024 ya nuna rashin tausayi.

Atiku ya ce gurfanar da yaran ya nuna gazawa wajen bin dokar da aka samar da niyyar kare matasan ƙasar nan.

"Abin ƙyama ne cewa ana azabtar da yara saboda nuna rashin jin daɗinsu da manufofin da suka shafi rayuwarsu kai tsaye."
"Ana iya auna ƙasa kan yadda take kula da ƴan ƙasarta masu rauni. Abin baƙin ciki ne cewa hatta yara masu ƙarancin shekaru ba su tsira daga muguntar T-Pain ba."

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya yi ƙus ƙus da sanatocin PDP 3 a Abuja, bayanai sun fito

- Atiku Abubakar

Shehu Sani ya ba Tinubu shawara

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon sanata mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani ya yi tir da yadda gwamnatin tarayya ta gurfanar da ƙananan yara gaban kotu.

Shehu Sani ya ce gwamnatin tarayya ta tafka abin kunya idan aka yi duba da karancin shekarun yaran da ake zargi da aikata laifi lokacin zanga-zanga.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng