'Yan Bindiga Sun Sake Kai Kazamin Hari, Sun Yi Garkuwa da Fasinjoji Sama da 20

'Yan Bindiga Sun Sake Kai Kazamin Hari, Sun Yi Garkuwa da Fasinjoji Sama da 20

  • Ƴan bindiga sun sake kai hari yankin Kontagora, sun yi garkuwa da fasinjoji akalla 22 a jihar Neja ranar Alhamis
  • Kakakin majalisar dokokin jihar Neja, Abdulmalik Sarkin Daji ya ce harin ya kara tabbatar da halin da ake ciki a Kontagora
  • Ɗan majalisa mai wakiltar Kontagora II, Abdullahi Isah ya koka kan yawaitar hare-haren ƴan bindiga a mazaɓarsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Niger - Rahotanni sun nuna akalla fasinjoji 22 ne ƴan bindiga suka yi awon gaba da su a yankin ƙaramar hukumar Kontagora da ke jihar Neja ranar Alhamis da ta shige.

'Yan bindigar dauke da muggan makamai sun tafi da fasinjojin, wadanda ke tafiya a cikin motoci biyar, zuwa dajin da ke kusa.

Kara karanta wannan

Kwana ya ƙare: Tsohon mataimakin shugaban majalisa ya rasu a hatsari

Gwamna Bago.
'Yan bindiga aun kuma sace mutane a yankin Kontagora a jihar Neja Hoto: Mohammed Umaru Bago
Asali: Twitter

Kakakin majalisar dokokin jihar Neja, Hon. Abdulmalik Sarkin Daji, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan bindiga sun tare matafiya a Kontagora

Ya ce miyagun sun yi garkuwa fasinjojin a daidai dajin Beri da ke kan titin zuwa Kontagora kusa da wani barikin soji.

Shugaban majalisar ya ce wannan harin ya kara tabbatar da maganar da ɗan majalisa mai wakiltar Kontagora II, Abdullahi Isah ya yi a kwanakin baya.

Tun farko dai Abdullahi Isah ya nuna fargaba kan yawaitar hare-haren da ‘yan bindiga ke kai wa kan titin Kontagora kusa da wani sansanin sojoji.

Karanta wasu labaran jihar Neja

Kara karanta wannan

Kaico: Wani matashin yaro ɗan shekara 16 ya hallaka kishiyar mahaifiyarsa

Yan bindiga sun kashe ƴan banga a Neja

A wani rahoton, kun ji cewa wasu miyagun ƴan ta'adda sun kai farmaki a jihar Neja inda suka hallaka jami'an tsaro na ƴan banga.

Ƴan ta'addan sun hallaka ƴan bangan ne a ƙaramar hukumar Mariga ta jihar a harin da suka kai ranar Alhamis, 31 ga watan Oktoban 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262