Zanga Zanga: Amnesty Ta Bukaci Tinubu Ya Gaggauta Sakin Yaran da aka Kai Kotu

Zanga Zanga: Amnesty Ta Bukaci Tinubu Ya Gaggauta Sakin Yaran da aka Kai Kotu

  • Kungiyar Amnesty International ta yi Allah wadai da yadda gwamnatin Bola Tinubu ta kama masu zanga zangar tsadar rayuwa
  • Amnesty ta buƙaci gwamnatin Bola Tinubu ta saki yaran da aka gurfanar a gaban kotun tarayya bisa zargin cin amanar kasa
  • Lamarin masu zanga zangar ya ja hankulan al'umma ne bayan gurfanar da su a kotu a cikin wani yanayi da yake nuna sun sha wuya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - An fara kira ga Bola Tinubu kan gurfanar da kananan yara da suka fito zanga zangar tsadar rayuwa.

Kungiyar Amnesty International a Najeriya ta bukaci sakin yaran cikin gaggawa ba tare da wani sharadi ba.

Kara karanta wannan

"Ana abin kunya:" Tsohon sanata ya ba Tinubu shawara kan shari'a da kananan yara

Tinubu
Amnestu ta bukaci sakin masu zanga zanga. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu|Amnesty International Nigeria
Asali: Twitter

Legit ta tattaro bayanan da Amnesty International ta yi ne a cikin wani sako da ta wallafa a shafinta na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Masu zanga zanga sun fadi a kotu

Yayin da aka gurfanar da yara masu zanga zangar, wasu daga cikinsu sun fadi a kasa saboda alamar yunwa da ke tattare da su.

Daily Trust ta wallafa cewa yara hudu daga cikin mutane 74 da aka gurfanar ne suka yanki jiki suka fadi a kasa yayin da yanayin sauran ke isar da sakon cewa sun sha azaba.

Amnesty ta bukaci sakin masu zanga zanga

Kungiyar Amnesty International ta buƙaci gwamnatin Bola Tinubu ta saki yaran da aka kama cikin gaggawa.

Amnesty ta ce gwamnatin Tinubu ba ta da wani dalilin cigaba da rike yaran saboda kawai sun fito zanga zanga.

"Gwamnati ta kulle su ba bisa ka'ida ba, ta gana musu azaba saboda kawai sun fito zanga zanga.

Kara karanta wannan

Zanga Zanga: Kananan yaran da aka kama sun sume a gaban alkali, an gano dalili

Muna kira ga gwamnatin Tinubu ta gaggauta sakinsu ba tare da wani sharadi ba.
Kokarin gurfanar da yaran a kan laifin cin amanar kasa ya nuna gwamnati ba ta bin doka kwata kwata."

- Amnesty International

Shehu Sani ya ce a saki yara da aka gurfanar

A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Shehu Sani ya sake dura a kan gwamnatin Bola Ahmed Tinubu bisa zargin aikata ba dai-dai ba ga yara ƙanana.

Tsohon Sanatan Kaduna ya fusata ne bayan wasu daga cikin yaran da gwamnati ke zargi da cin amanar kasa sun fadi a kotu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng