"Na Azabtu:" Mai Zanga Zanga Ya Fadi Yadda Ya Shafe Kwanaki 60 a Hannun DSS
- Daya daga cikin wadanda su ka yi zanga-zanga a Kano ya fadi irin wahalar da ya sha a hannun jami'an tsaron DSS
- Khalid Aminu ya bayyana cewa bai taba shan azaba irin wacce ya sha a hannun jami'an har na tsawon watanni
- Khalid ya na daga cikin tarin matasan da aka kama a Kano bisa zargin daga tutar Rash yayin zanga-zangar lumana
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Khalid Aminu, daya daga cikin wadanda su ka fito zanga zangar adawa da yunwa a watan Agusta ya shaki iska bayan kwanaki 60 a hannun DSS.
Khalid, wanda jami'an tsaron su ka dauka daga jihar Kano a zanga zangar Agusta ya ce ya sha bakar wahala lokacin da ya ke tsare.
A hira da ta kebanta da Channels Television, Khalid Aminu ya ce babu irin azabar da jami'an DSS ba su ganawa masu zanga zanga da aka kama ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Na sha azaba a wajen DSS:" Khalid
Matashin Injiniya, Khalid Aminu ya ce jami'an DSS da su ka kama shi a Kano sun tsare shi ba tare da ba ba damar ganawa da yan uwa ko abokansa ba.
Ya ce tashin farko, jami'an DSS sun rika dukansu da wata bulala mai kauri, sannan aka ce su kwanta a kan ciyawa mai kaifi, su na birgima ana watsa masu ruwa.
Hukumar DSS ta gana masa azaba
Matashin mai zanga-zanga, Khalid Aminu ya ce daga baya jami'an DSS sun umarce su da su rika rarrafe a cikin kwata, sannan an sa su kallon rana.
Ya ce zargin da jami'an DSS ke masu na daga tutar Rasha yayin zanga-zangar ba gaskiya ba ne, amma duk da haka sai da aka masu dukan kawo wuka.
DSS sun kama shugaban masu zanga zanga
A wani labarin mun ruwaito cewa jami'an tsaron farin kaya na DSS sun kama guda daga cikin jagororin masu gudanar da zanga-zanga.
An samu rahoton kama Micheal Lenin a gidansa da ke Apo a Abuja, tare da gana masa azaba a gaban iyalansa kafin jami'an su yi awon gaba da shi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng