Ba Ƙabilanci a Musulunci: Sheikh Jingir Ya Tura Sako ga Tinubu
- Shugaban malaman ƙungiyar Izala mai hedikwata a Jos ya yi kira na musamman ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu
- Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir ya bukaci Bola Tinubu ya yi dubi kan rikicin siyasa da ya ke faruwa a jihohin Rivers da Kano
- Malamin ya kuma yi magana kan matsalar lantarki da aka shiga a Arewacin Najeriya inda aka shafe kwanaki goma ba wuta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Fitalo - Shugaban malaman Izala, Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir ya tura sako ga Bola Tinubu.
Sheikh Sani Yahaya Jingir ya bukaci Bola Tinubu ya yi bincike kan wasu abubuwa da suke faruwa a Najeriya.
Legit ta tatttaro bayanan da Sheikh Jingir ya yi ne a cikin wani bidiyo da Hamza Muhammad Sani ya wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sakon Sheikh Jingir ga Bola Tinubu
Sheikh Jingir ya bukaci shugaba Tinubu ya yi bincike kan rikicin siyasa da yake faruwa a jihohin Rivers, Kano da Filato.
Shugaban malaman ya ce addinin Musulunci bai yarda da kabilanci, rashin gaskiya ko saɓa alkwari ba.
"Bai kamata gwamnan da ya gama shekaru takwas ya zo ya hana wanda ya biyo bayansa aiki ba.
Kada a bari a tayar da rikici a jihohin Rivers da Kano saboda wasu tsofaffin gwamnoni suna tare da gwamnati.
Ina kira ga shugaba Tinubu ya yi bincike a kan abin da ke faruwa a Kano da jihar Rivers domin tabbatar da gaskiya da adalci.
- Sheikh Jingir
Sheikh Jingir ya yi magana kan lantarki
Sheikh Sani Yahaya Jingir ya ce rashin wuta da aka shiga a Arewa na da alaƙa da sakacin shugabannin da suka fito daga yankin.
Malamin ya kuma yi kira ga Bola Tinubu ya binciki me ya saka wasu gwamnoni shigar da EFCC kotu domin tabbatar da gaskiya.
Malamai sun goyi bayan APC
A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar malaman addinin Musulunci a jihar Ondo ta goyi bayan gwamna Lucky Aiyedatiwa.
Malaman sun ce za su zabi jam'iyyar APC a zaben gwamna da za a yi a jihar Ondo kamar yadda suka zabi Bola Ahmed Tinubu.
Asali: Legit.ng