Shugaban Malamai Ya Dauki Alkawarin Tallata Ɗan Takarar APC
- Gwamnan Ondo, Lucky Aiyedatiwa ya yi wata ganawa da shugabannin Musulunci yayin da zaben jihar ke kara matsowa.
- Malaman Musulunci a jihar Ondo sun ce kamar yadda suka goyi bayan Bola Tinubu za su kara goyon bayan Aiyedatiwa
- Gwamna Aiyedatiwa ya yi alkawarin tafiya tare da dukkan al'ummar jihar Ondo idan Allah ya ba shi nasara a zaben bana
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Ondo - Yayin da ake fuskantar zaben Ondo, Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya gana da malaman addinin Musulunci.
Malaman addini a jihar Ondo sun amince da goyon bayan gwamna Lucky Aiyedatiwa bayan ganawa.
Legit ta tattaro bayanan da malaman suka yi ne a cikin wani sako da hadimin gwamnan Ondo, Ebenezer Adeniyan ya wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Malamai sun goyi bayan dan takarar APC
Kungiyar hadin kan malaman addinin Musulunci ta jihar Ondo ta yi alkawarin mara baya ga gwamna Lucky Aiyedatiwa.
A ranar 16 ga Nuwamba hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) za ta gudanar da zaben gwamna a jihar Ondo.
Leadership ta wallafa cewa shugaban malaman jihar Ondo Sheikh Ahmad Olagoke Aladesawa ya ce dukkansu za su goyi bayan gwamna Aiyedatiwa.
'Bisa lura da goyon bayan da muka nuna masa, gwamna Aiyedatiwa zai iya komawa gida ya yi barci domin nasara ta shi ce.
- Sheikh Abdulhakeem Yayi Akorede, babba limamin Akure
Bayanin gwamnan jihar Ondo
Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya bayyana cewa a yanzu haka akwai musulmai da dama da ke rike da mukamai a gwamnatinsa.
Bayan haka, gwamnan ya kara da cewa zai cigaba da damawa da al'ummar Musulmi a jihar Ondo idan Allah ya ba shi nasara.
Haka zalika gwamnan ya mika godiya da al'ummar Musulmi bisa nuna masa goyon baya da suka yi.
Sarki ya goyi bayan dan takarar APC
A wani labarin, mun ruwaito muku cewa mai martaba Oba Olufaderin Adetimehin ya ce zai goyi bayan mai girma gwamna Lucky Aiyedatiwa.
Oba Olufaderin Adetimehin ya ce zai umarci dukkan mutanen yankinsa su zabi gwamna kuma dan takarar APC a zaɓen Ondo mai zuwa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng