"Ana Abin Kunya:" Tsohon Sanata Ya Ba Tinubu Shawara kan Shari'a da Kananan Yara

"Ana Abin Kunya:" Tsohon Sanata Ya Ba Tinubu Shawara kan Shari'a da Kananan Yara

  • Sanata Shehu Sani ya sake dura a kan gwamnatin Bola Ahmed Tinubu bisa zargin aikata ba dai-dai ba ga yara ƙanana
  • Tsohon Sanatan Kaduna ya fusata ne bayan wasu daga cikin yaran da gwamnati ke zargi da tarzoma sun fadi a kotu
  • A ranar Juma'a ne aka gurfanar da wasu yara da jami'an rundunar yan sandan kasar nan su ka kama gaban babbar kotun tarayya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna - Tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani ya yi tir da yadda gwamnatin tarayya ta gurfanar da kananan yara gaban kotu. Ya ce gwamnatin tarayya ta tafka abin kunya idan aka yi duba da karancin shekarun yaran da ake zargi da aikata laifi lokacin zanga-zanga.

Kara karanta wannan

An tashi baram baram: Gwamnati da ma'aikatan jami'o'i sun gaza fahimtar juna

Tinubu
Shehu Sani ya caccaki gwamnati bayan kai yara kotu Hoto: @Nwafresh/@AmnestyNigeria
Asali: Twitter

A sakon da ya wallafa a shafinsa na X, Shehu Sani ya shawarci mahukuntan kasar nan kan abin da ya dace su yi da yaran da ake tuhuma da karya doka.

"Gwamnati ta yi abin kunya:" Tsohon Sanata

Tsohon Sanata Shehu Sani ya ce gurfanar da yara masu karancin shekaru da gwamnatin Najeriya ta yi a gaban kotu babbar abin kunya ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Shehu Sani ya kara da cewa wannan abu da ya afku tamkar cin mutuncin dimokuradiyya ne da bai dace a samu gwamnati da aikatawa ba.

Tsohon Sanata ya ba Tinubu shawara

Tsohon Sanata Shehu Sani ya shawarci gwamnatin tarayya da ta gaggauta janye zarge-zargen da ta ke yi wa yaran da aka kama lokacin zanga-zanga.

Ya kuma kara shawartar gwamnati da ta tabbatar da an mayar da dukkanin yaran gaban iyayensu a jihohin da aka dauko su.

Kara karanta wannan

Matsalar Arewa ta fito fili, Mahdi Shehu ya tona wadanda suka saida al'umma

Gwamnatin Tinubu ta gurfanar da yara kotu

A wani labarin kun ji cewa wasu daga cikin yara masu karancin shekaru da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta gurfanar a gaban kotu sun suma ana shari'a.

Yaran wadanda rundunar yan sanda ta kamo daga jihar Kano sun yanke jiki sun fadi, lamarin da lauyansu ya ce ya nuna ba sa samun abinci a hannun yan sanda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.