An Tashi Baram Baram: Gwamnati da Ma'aikatan Jami'o'i Sun Gaza Fahimtar Juna

An Tashi Baram Baram: Gwamnati da Ma'aikatan Jami'o'i Sun Gaza Fahimtar Juna

  • An sake tashi babu fahimtar juna tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar ma'aikatan jami'o'i da ke yajin aiki
  • Kungiyar ma'aikatan ta fara yajin aiki a ranar Litinin, inda ta zargi gwamnati da kin daukar hakkokinsu da muhimmanci
  • Shugaban SSANU na kasa, Mohammed Ibrahim ya ce ba za su koma bakin aiki ba sai gwamnati ta biya albashinsu da ta rike

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Gwamnatin tarayya da gamayyar kungiyar ma'aikatan Najeriya sun gaza cimma matsaya domin kawo karshen yajin aikin da ake yi.

Tsohon karamin Ministan ilimi, Dr Yusuf Sununu ne ke jagorantar tattaunawar da zummar samar da daidaito tsakanin ma'aikatan da gwamnati.

Kara karanta wannan

"Ana abin kunya:" Tsohon sanata ya ba Tinubu shawara kan shari'a da kananan yara

Ilimi
Gwamnati da kungiyar malamai sun gaza kawo karshen yajin aiki Hoto: Federal Ministry of Education
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta ruwaito cewa duk da zaman da aka yi a ranar Alhamis, gwamnati ta kasa biyawa ma'aikatan bukatunsu ballantana su janye yajin aiki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ma'aikatan jami'o'i sun shiga yajin aiki

A ranar Litinin ne kungiyoyin ma'aikatan jami'o'i na SSANU da NASU su ka tsunduma yajin aiki bisa rike masu albashin wata hudu da gwamnati ta yi.

Amma a sakon da gwamnati ta wallafa a shafin ma'aikatar ilimi na Facebook,ta ce a shirye ta ke wajen kawo karshen yajin aikin ma'aikatan.

Yaushe ma'aikata za su janye yajin aiki?

Shugaban kungiyar SSANU na kasa, Mohammed Ibrahim ya bayyana cewa manyan ma'aikatan jami'o'i har da shugabanninsu ba su karbi albashi ba.

Mohammed Ibrahim ya ce za su cigaba da kulle manyan makarantun kasar nan har sai sun ga albashinsu na wata hudu ya nuna a akawun.

Kara karanta wannan

Ma'aikata za su fuskanci matsala, za a samu jinkirin albashin wasu watanni

Ma'aikatan jami'o'i sun ki komawa aiki

A baya mun ruwaito cewa kungiyar ma'aikatan jami'o'i ta ce babu abin da zai mayar da ita bakin aiki matukar gwamnatin tarayya ba ta biya hakkokinsu ba.

Shugaban kungiyar SSANU na kasa, Mohammed Ibrahim ya ce abin takaici ne yadda gwamnati ke masu wasu da hankali game da inda albashinsu ya makale.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.