Ma'aikata za Su Fuskanci Matsala, Za a Samu Jinkirin Albashin Wasu Watanni
- Wasu ma'aikatan hukumomi da ma'aikatu da cibiyoyin gwamnatin tarayya 17 za su fuskanci matsala wajen albashi
- Biyan mafi ƙarancin albashin akalla N70,000 da ma'aikatantun su ka yi ya sa sun kashe duka kuɗin da aka ware masu
- Wannan na nufin za a samu jinkirin biyan albashin watannin ukun ƙarshen 2024 da su ka hada da Oktoba, Nuwamba da Disamba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Wani bincike ya bankaɗo matsala a biyan albashin ma'aikatan kasar nan, inda ake fargabar samun jinkirin biyan haƙƙoƙinsu.
Matsalar za ta shafi ma'aikatan cibiyoyi, ma'aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya 17 saboda wata tangarda da aka samu.
Jaridar Punch ta gano cewa ma'aikatun da hukumomin gwamnati sun kashe kuɗin da aka ware masu a kan biyan ma'aikata bayan tabbatar da sabon albashi N70,000.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka gano shirin jinkirta biyan ma'aikata
Wata sanarwa da aka aika ga ma'aikatan Voice of Nigeria ce ta bayyana sabon bayanin samun jinkirin biyan ma'aikatan albashi su.albashinsu.
Daraktan kuɗi ne ya fitar da sanarwar a madadin darakta janar na kamfanin, Jack Odeh, inda inda aka ce ana duba wasu hanyoyin biyan albashin.
A waɗanne watanni za a jinkirta albashi?
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ma'aikatan wasu ma'aikatu da hukumomi 17 ba za su samu albashinsu na watanni uku da wuri ba.
Za a samu jinkirin ne a watanni Oktoba, Nuwamba da Disamba a shekarar 2024 bayan fara biyan mafi ƙarancin albashi.
Gwamna zai biya mafi ƙarancin albashi
A wani labarin mun ruwaito cewa gwamnatin jihar Kaduna ta amince da biyan ma'aikatanta mafi ƙarancin albashin N72,000 bayan NLC da gwamnatin tarayya sun cimma matsaya.
Gwamna Malam Uba Sani ne ya tabbatar da haka, kuma za a fara biyan N72,000 a watan Nuwamba tare da jigilar ma'aikata kyauta daga wuraren aiki saboda saukaka tsadar rayuwa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng