Ganduje Ya Nemawa Gwamna Mai Barin Gado Alfarma, Ya Nemi a Hakura Da Bincikensa
- Shugaban APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya ba zaɓaɓɓen gwamnan Edo, Monday Okpebholo shawarwari
- Daga cikin abubuwan da ya faɗa masa, ya ce bibiyar gwamnatin baya domin bincikenta ba shi zai kawo cigaba ba
- Zaɓaɓɓen gwamnan, Sanata Monday Okpebholo ya godewa Ganduje bisa ƙoƙarin da ya yi har APC ta yi nasara kan PDP
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Edo - Shugaban APC na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya nemawa gwamnan APC mai barin gado a jihar Edo, Godwin Obaseki alfarma.
Dakta Ganduje, wanda shi kansa ke fuskantar bincike kan almundahana a jihar Kano, ya roƙi zaɓaɓɓen gwamnan Edo, Monday Okpebholo da kar ya binciki Obaseki .
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Abdullahi Ganduje ya nemi alfarmar ne a lokacin da Monday Okpebholo ya ziyarci ofishin APC na ƙasa a Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ganduje ya shawarci Okpebholo kan Edo
Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya shawarci Sanata Monday Okpebholo bisa yadda zai gudanar da jihar.
Dakta Ganduje, wanda shi ne shugaban APC na ƙasa ya shawarci zaɓaɓɓen gwamnan Edo ya mayar da hankali wajen kawo ayyukan cigaba ga jama'arsa.
Ganduje ya yabi zaɓaɓɓen gwamnan Edo
Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana yaƙinin APC na cewa gwamna Monday Okpebholo zai yi wa mutanensa na jihar Edo aiki.
A martaninsa, Sanata Okpebholo ya ce zuwan Abdullahi Ganduje jihar Edo ya taka muhimmiyar rawa wajen nasarar da ya samu a matsayin gwamna.
Gwamna ya caccaki masu sukar ziyarar Ganduje
A baya kun ji cewa gwamnan jihar Nassarawa, Abdullahi Sule ya ce bai ga wani abin surutu ba saboda ya ziyarci shugaban jam'iyyar APC na kasa, Dakta Abdullahi Ganduje.
Gwamna Sule, wanda shi ne shugaban gwamnonin APC na shiyyar Arewa ya ce ya ziyarci Ganduje ne bayan ya tura masa goron gayyata domin tattauna muhimman batutuwa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng