Kwastam Ta Damke Fetur na Miliyoyin Kudi ana Shirin Safararsa zuwa Ketare

Kwastam Ta Damke Fetur na Miliyoyin Kudi ana Shirin Safararsa zuwa Ketare

  • Hukumar kwastam ta kasa ta kama lita mai yawa ta man fetur da ake shirin safarsa zuwa kasar waje ta iyakar Najeriya da Kamaru
  • Wannan ya sa aka kama su, inda aka ga masu safarar da buhunan shinkafa yar waje da ake shirin fita da su yayin da yan ksar nan ke kuka
  • Shugaban hukumar kwastam da ke kula da jihohin Adamawa da Tarana, Garba Bature ya ce za su zage damtse wajen yakar masu aika-aika

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Adamawa – Jami’an hukumar kwastam ta kasa ta yi nasarar kama masu so raba Najeriya da fetur da ya kai N71,760,930 idan ya shiga kasuwa.

Kara karanta wannan

"Kar ku ji komai:" Yan kasuwa sun yi martani bisa fargabar karancin fetur

Jami’an hukumar sun yi babban kamen a iyakar jihar Adamawa inda wasu da ake zargin ba sa kishin kasa ke kokarin safarar fetur zuwa kasar Kamaru.

fetur
An kama man fetur a hanyar fitar da shi daga Najeria Hoto: Nigeria Customs Service
Asali: Facebook

Tashar TVC Television ta wallafa cewa baya ga jarkokin man fetur, jami’an kwastam sun yi ram da buhunan shinkafa ‘yar gwamnati.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kayayyakin da kwastam ta kama a Adamawa

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa jami’an kwastam sun kama duro 26 makare da man fetur, kuma kowane duro na dauke da litar fetur 220 da jarkoki mai daukar lita 25 guda 1,115, duk cike da fetur.

Jami’an sun kara da kama buhuna 200 na fulawa masu nauyin kilo 50, shinkafa ‘yar waje buhu 57 da dila 10 ta gwanjo.

Kwastam za ta kara jajircewa wajen kame

Shugaban hukumar kwastam da ke kula da jihohin Adamawa da Tarana, Garba Bature ya ce jami’ansu za su saka kafar wando daya da masu safarar kaya ba bisa ka’ida ba.

Kara karanta wannan

Hatsarin jirgi: An samu karin gawar ma'aikacin NNPCL bayan kwanaki

Ya kara da cewa za su cigaba da mutunta dokokin aiki tare da hana masu fasakwauri a kasar nan sakat har sai an tsaftace iyakokin Najeria.

Jami’an kwastam sun kama kaya

A baya mun ruwaito cewa jami’an hukumar kwastam na kasa sun yi nasarar dakile mummunan al’amari bayan sun yi ram da tulin wasu mugayen makamai da ake kokarin shigowa da su.

Shugaban hukumar kwastam, Adewale Adeniyi ya kara da cewa a rahoton da aka fitar na makaman da jami’ansu suka cafke a cikin shekaru shida, kudinsu ya kai akalla Naira biliyan 9.5.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.