Gwamnoni Sun Fusata, Sun Gayyaci Shugaban NNPCL kan Matsalar Fetur

Gwamnoni Sun Fusata, Sun Gayyaci Shugaban NNPCL kan Matsalar Fetur

  • Gwamnonin Najeriya ta yi takaicin yadda ƙasar nan ke cigaba da sayo man fetur duk da tarin danyen mai a cikin gida
  • Kungiyar ƙarƙashin jagorancin gwamnan Imo, Hope Uzodinma ta zauna da shugaban NNPCL, Mele Kyari kan tsadar fetur
  • Gwamnonin sun ce dole ne ta taimakawa gwamnatin tarayya domin gyara matatun mai ko za a samu sauƙin matsalar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Gwamnonin jihohin Najeriya 36 sun yi tir da yadda matsalar fetur ta ƙi ci ta ƙi cinyewa duk da albarkar mai da ke danƙare a ƙasar.

Ƙungiyar a inuwar 'Progressive Governors Forum' ta yi mamakin ƙamarin da matsalar fetur ke yi a Najeriya duk da cewa ta na cikin manyan ƴan ƙungiyar OPEC.

Kara karanta wannan

Gwamnonin jihohi sun gana a Abuja kan muhamman batutuwa 4, bayanai sun fito

Gwamna
Gwamnoni sun yi tir da matsalar fetur Hoto: Babatunde Muhammadu Quadri
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa shugaban kungiyar gwamnonin kuma gwamnan Imo, Hope Uzodinma ya ce bai ga dalilin da ƙasar nan za ta riƙa shigo da fetur daga ƙetare ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matsalar fetur: Gwamnoni sun zauna da NNPCL

Kungiyar gwamnonin kasar nan ta gayyaci shugaban kamfanin mai na ƙasa (NNPCL), Mele Kyari domin samun bayanin halin da sashen fetur ke ciki.

Gwamnonin sun nemi bahasin inda aka kwana wajen wadata ƴan Najeriya da fetur a cikin farashi mai rahusa domin rage wahalar da ake ciki.

Gwamnoni na neman mafitar tsadar fetur

Gwamnonin jihohin kasar nan sun ce dole su bayar da ta su gudunmawar wajen kawo karshen matsalar man fetur da ta shafe shekaru ana fama.

Shugaban kungiyar gwamnonin, Hope Uzodinma ya ce za su bayar da goyon baya wajen ganin gwamnati ta kammala gyara matatun mai na cikin gida.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya shiga ganawa da Aliko Dangote, an samu bayanai

"Akwai fetur a ƙasa:" MEMAN

A baya mun wallafa cewa kungiyar masu kasuwancin man fetur ta MEMAN ta musanta cewa za a samu ƙarancin man fetur yayin da NNPCL ta kara farashi.

Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Kwamred Clement Isong ne ya bayar da tabbacin, sannan ya shawarci mutane su daina sayen fetur su na ɓoyewa saboda mai ya wadata.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.