Kaico: Wani Matashin Yaro Ɗan shekara 16 Ya Hallaka Kishiyar Mahaifiyarsa

Kaico: Wani Matashin Yaro Ɗan shekara 16 Ya Hallaka Kishiyar Mahaifiyarsa

  • Yan sanda sun damke yaro ɗan shekara 16, Nuhu Haruna bisa zargin hallaka kishiyar mahaifiyarsa a yankin Dutsinma a Katsina
  • Kakakin ƴan sandan jihar, ASP Abubakar Sadiq ya ce an kama wanda ake zargin ne bayan ya bugawa matar sanda a ciki, daga bisani ta rasu
  • Ya ce ƴan sanda sun kuma cafke Abubakar Nasiru bisa zargin haɗa baki da kuma garkuwa da mutane a yankin ƙaramar hukumar Kafur

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Katsina - Rundunar ƴan sanda reshen jihar Katsina ta cafke wani karamin yaro ɗan kimanin shekara 16, Nuhu Haruna bisa zargin kashe kishiyar mahaifiyarsa.

Rundunar ta kuma kama wasu mutane da ake zargi da aikata mugayen laifuka kamar garkuwa da mutane, fashi da makami da sauransu a jihar Katsina.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka mutane masu yawa a mahaifar tsohon gwamna

Sufetan yan sanda.
An kama wani karamin yaro bisa zargin kashe kishiyar mahaifiyarsa a Dutsinma Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar, ASP Abubakar Sadiq, ne ya bayyana haka a lokacin da yake nuna waɗanda ake zargin, Punch ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda matashin yaro ya kashe gwaggwonsa

Ya ce ƴan sanda sun kama Nuhu Haruna ne bayan wata mummunar hatsaniya da suka yi da kishiyar mahaifiyarsa, Rabi Haruna mai shekaru 40, wanda ya yi sanadin mutuwarta.

"A ranar 21 ga Oktoba, 2024, da misalin karfe 1:00 na rana, ‘yan sanda suka kama wani yaro, Nuhu Haruna, mai shekaru 16 a kauyen Fenza da ke karamar hukumar Dutsinma, bisa laifin kisan kai.
“An ruwaito cewa wanda ake zargin ya bugi kishiyar mamarsa da sanda a cikinta a lokacin da suka samu saɓani, wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwarta."

Yan sanda sun kama mai garkuwa da mutane

Ƴan sandan sun kuma tsare wani, Abubakar Nasiru wanda aka fi sani da Haro dan karamar hukumar Daura bisa zarginsa da hannu a ayyukan garkuwa da mutane.

Kara karanta wannan

An kama dan bindigar da ya kashe basarake bayan karɓar miliyoyi

A ruwayar Channels tv, kakakin ƴan sandan ya kara da cewa:

"Abubakar Nasiru ya hada baki da wasu a 2023, inda suka kai hari kauyen Unguwar Maza dake karamar hukumar Kafur, suka sace mutane uku.
"Sai da aka biya kudin fansa naira miliyan 13 domin sako su, kuma Abubakar ya amince ya karbi Naira miliyan 2 a matsayin kasonsa."

An kama mai kaiwa ƴan bindiga makamai

A wani rahoton an ji cewa asirin wani mai sayen makami da kayan fada ga yan bindiga masu garkuwa da mutane ya tonu a jihar Katsina da ke Arewacin Najeriya.

Yan sa kai a jihar Katsina sun kama tulin harsashi yayin da mugun mutumin ya ɓoye su a cikin wata motar haya da yake tafiya Batsari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262