'Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane Masu Yawa a Mahaifar Tsohon Gwamna
- Wasu miyagun ƴan bindiga sun kai hari a garin Anyiin da ke ƙaramar hukumar Logo ta jihar Benue
- Ƴan bindigan waɗanda suka shafe kusan sa'o'i suna aikata ta'asa, sun hallaka mutane masu yawa tare da raunata wasu da dama
- Wani jami'an gwamnati da ya tabbatar da aukuwar harin ya bayyana cewa an tura jami'an tsaro zuwa yankin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Benue - Rahotanni sun ce an kashe mutane da dama a wani sabon hari da ƴan bindiga suka kai a garin Anyiin da ke ƙaramar hukumar Logo ta jihar Benue.
Ƴan bindigan sun mamaye garin ne a ranar Laraba da misalin ƙarfe 6:32 na yamma, inda suka kashe mutane da dama.
Jaridar The Punch ta ruwaito cewa wasu da dama sun samu raunuka daban-daban, yayin da aka ba da rahoton ɓacewar mutane masu yawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Garin Anyiin dai nan ne mahaifar tsohon gwamnan jihar Benue, Gabriel Suswam.
Yadda ƴan bindiga suka kai harin
Wani shugaban al’umma daga Anyiin, Joseph Anawah, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Alhamis, ya ce ƴan bindigan waɗanda sun haura 20 ɗauke da muggan makamai, sun shafe sa'o'i uku a yayin harin.
"A jiya Laraba, 30 ga Oktoba, 2024, ƴan bindiga sun kai hari garin Anyiin da ke ƙaramar hukumar Logo ta jihar Benue da misalin ƙarfe 6:32 na yamma."
"A yayin harin sun kashe sama da mutane 15, wasu sun samu raunuka sannan wasu kuma sun ɓace."
- Joseph Anawah
Me hukumomi suka ce kan lamarin?
Da aka tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Catherine Anene, ta ce har yanzu ba ta samu rahoton faruwar lamarin ba.
Mai ba gwamnan jihar shawara na musamman kan harkokin tsaro, Alex Igbaya, ya tabbatar da faruwar lamarin amma ya ki bayar da adadin mutanen da suka mutu.
"An riga an tura jami’an tsaro yankin, sojoji suna can."
- Alex Igbaya
Ƴan bindiga sun sace manoma
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga sun yi garkuwa da aƙalla mutane 16 a wani hari a jihar Kebbi da ke yankin Arewa maso Yamma.
Ƴan bindigan sun sace mutanen ne a wani hari da suka kai ƙauyen Bena da kewaye a ƙaramar hukumar Danko/Wasagu ta jihar Kebbi.
Asali: Legit.ng