Gwamna Uba Sani Ya Amince da Sabon Mafi Karancin Albashi ga Ma'aikatan Kaduna

Gwamna Uba Sani Ya Amince da Sabon Mafi Karancin Albashi ga Ma'aikatan Kaduna

  • Gwamnan Kaduna, Malam Uba Sani ya sanar da sabon mafi ƙarancin albashi ga ma'aikatan gwamnatin jihar
  • Uba ya amince da N72,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi ga ma'aikata wanda za a fara aiwatarwa daga watan Nuwamban 2024
  • Hakazalika Gwamnan zai ƙaddamar da shirin fara jigilar ma'aikatan gwamnati wajen zuwa da dawo daga wuraren aikinsu kyauta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya amince da sabon mafi ƙarancin albashi ga ma'aikatan jihar.

Gwamna Uba Sani ya amince da N72,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi ga ma’aikatan jihar Kaduna daga watan Nuwamba 2024.

Uba Sani ya amince da mafi karanci albashi
Uba Sani ya amince da mafi karancin albashin N72,000 Hoto: @ubasanius
Asali: Twitter

Uba Sani zai biya albashin N72,000 a Kaduna

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaran gwamnan Kaduna, Ibrahim Musa ya fitar, cewar rahoton tashar Channels tv.

Kara karanta wannan

Lokaci ya yi: Tsohon mataimakin gwamna a Najeriya ya rasu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa matakin ya yi daidai da ƙudirin gwamnatin Uba Sani na kare muradun ma’aikata da inganta rayuwar talakawa da marasa galihu a jihar Kaduna, rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar.

Haka kuma ya yi daidai da jajircewar Gwamna Uba Sani wajen ingantawa da kare haƙƙin ma’aikata, inganta jin daɗinsu, da kula da talakawa da marasa ƙarfi.

Bugu da ƙari, sanarwar ta ce Gwamna Uba Sani na shirin ƙaddamar da shirin sufuri na kyauta ga ma’aikatan gwamnati.

Za a ƙaddamar da shirin ne ta hanyar sakin motoci 100 masu amfani da gas na CNG domin jigilar ma'aikata.

Motocin, a cewar mai magana da yawun Gwamna Uba Sani, za su riƙa jigilar ma’aikatan gwamnati wajen zuwa da dawowa daga aiki.

Gwamna ya yi ƙoƙari

Wata malamar makaranta a jihar Kaduna mai suna Saida Nasir ta shaidawa Legit Hausa cewa gwamnan ya yi ƙoƙari ta hanyar amincewa da sabon mafi ƙarancin albashin.

Kara karanta wannan

Ma'aikata za su fuskanci matsala, za a samu jinkirin albashin wasu watanni

"Eh to abin a yaba ne domin ko ba komai an samu ƙari kuma za a ɗan rage wasu abubuwan duk da cewa ba za su isa ba."

- Saida Nasir

Karanta wasu labaran kan mafi ƙarancin albashi

Gwamnan Ebonyi zai biya albashin N75,000

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan Ebonyi, Francis Nwifuru, ya bayyana mafi ƙarancin albashin da zai biya ma'aikatan jihar.

Gwamna Francis Nwifuru ya amince da biyan N75,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi ga ma'aikatan jihar wanda za a fara aiwatarwa daga watan Oktoban 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng