'A Bar Mutane Su Mallaki Bindiga domin Maganin Yan Ta'adda,' Sanata

'A Bar Mutane Su Mallaki Bindiga domin Maganin Yan Ta'adda,' Sanata

  • Sanata Ned Nwoko ya cigaba da goyon bayan ra'ayin ba yan kasa damar mallakar makamai domin kare kansu daga sharrin yan bindiga
  • Ned Nwoko ya bayyana cewa ba yan Najeriya damar mallakar makami na cikin hanya mafi sauki da za a kawo karshen yan ta'adda
  • Sai dai Sanatan ya yi karin haske kan sharudan da suka zama wajibi mutum ya cika kafin samun damar mallakar makami a kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Sanata mai wakiltar Delta ta Arewa ya cigaba da kira kan ba yan Najeriya damar mallakar makami.

Ned Nwoko ya ce idan aka bi ƙa'ida wajen ba jama'a damar mallakar makami za a rage matsalolin yan bindiga masu garkuwa da mutane.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun ƙona gawar ɗan kasuwa bayan harbe shi har lahira

Sanata Ned
Sanata ya bukaci a ba mutane damar mallakar makami. Hoto: Ned Nwoko
Asali: UGC

Sanatan ya yi magana ne a wata hira da ya yi da gidan Talabijin din Channels a kan siyasa da lamuran yau da kullum.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Ya dace mutane su mallaki bindiga' - Sanata Nwoko

Vanguard ta wallafa cewa Sanata Ned Nwoko ya ce ya kamata yan Najeriya su mallaki bindiga domin kare kansu daga sharrin yan ta'adda.

Nwoko ya bayyana cewa idan mutane suka mallaki makami za su samu damar kare kansu kuma hakan zai rage matsalar yan ta'adda.

"A Nuwamban 2023 wasu yan bindiga sun shiga gidan babban ma'aikacin majalisa suka yi garkuwa da shi.
Da a ce yana da bindiga ko mutanen unguwa suna da makami da hakan bai faru ba, za su tunkari yan ta'addar.
Idan da masu garkuwa da mutanen sun san yana da bindiga ko gidansa ba za su isa ba."

Kara karanta wannan

‘Ba a son ranmu ba ne': Mabarata ga Ministan Tinubu da yake shirin fatattakarsu

- Sanata Ned Nwoko

Nwoko ya fadi sharudan mallakar bindiga

Sanata Ned Nwoko ya bayyana cewa kafin a ba mutum damar mallakar bindiga ya kamata a koya masa harbi kuma dole a tabbatar yana da lafiya.

Nwoko ya kara da cewa bayan tabbatarwa daga yan sanda sai hakimi ko mai unguwar yankin mutum yana da masaniya.

Dikko Radda zai ba mutane bindiga

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya nuna takaici kan yadda yan bindiga ke kashe mutane da sace su a Arewacin Najeriya.

Dikko Umaru Radda ya ce a shirye yake ya ba mutane bindigogi domin su rika fafatawa da yan ta'adda masu garkuwa da mutane a Katsina.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng