Rashin Lantarki: Yan Arewa Sun Tafka Asara, An Rasa Sama da Naira Tiriliyan 1

Rashin Lantarki: Yan Arewa Sun Tafka Asara, An Rasa Sama da Naira Tiriliyan 1

  • Kungiyar kare hakkin dan Adam ta International human rights commission (IHRC) ta ce an yi asara mai nauyi a Arewa
  • Shugaban hukumar reshen Najeriya, Ambasada Abdullahi Bakoji ne ya bayyana haka a sanarwar da ya fitar a jihar Kano
  • Ya kuma kara tabbatarwa Legit cewa matsalar lantarkin Arewa ta jawo asarar akalla Naira tiriliyan 1.5 a cikin kwanakin nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Hukumar kare hakkin dan Adam ta International human rights commission (IHRC) ta ce yan Arewa sun tafka mummunan asara saboda rashin wuta.

Shugaban hukumar na Najeriya, Ambasada Abdullahi Bakoji ne ya fadi haka yayin da aka fara ganin kyallin wutar lantarki a shiyyar.

Kara karanta wannan

Sanata ya tada hankalin Gwamna Abba, ya ce jam'iyyar APC za ta ƙwace Kano a 2027

Transmission
Rashin lantarki ya jawo asarar N1.5tn a Arewa Hoto: Transmission Commission of Nigeria
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Ambasada Bakoji ya ce asarar da aka tafka ta haura biliyoyin Naira, ta doshi tiriliyan biyu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An yi asarar Tiriliyoyi saboda wutar Arewa

Ambasada Abdullahi Bakoji ya tabbatar da cewa Arewa ta yi asarar Naira Tiriliyan 1.5 daga 9 Satumba, 2024 zuwa yanzu.

Ambasada Bakoji ya ce jimawa da Arewacin Najeriya ta yi a cikin duhu ya tauye hakkin dan Adam na mazauna shiyyar.

IHRC ta fadi matsalar rashin wuta a Arewa

Hukumar kare hakkin dan Adam ta bayyana cewa rashin wutar lantarki a Arewa ya kara dagula harkokin tsaron da ake fama da shi a yankin.

Shugaban hukumar reshen Najeriya, Ambasada Abdullahi Bakoji ya ce an tauye hakkin jama'a matuka yayin da aka jefa rayuwarsu a cikin rashin tabbas.

Ya shawarci gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da ta gaggauta samar da hanyar magance matsalar lantarki, ba wai na dan lokaci kawai ba.

Kara karanta wannan

Dan majalisar kano ya jero illolin rashin wuta a arewa, ya ga gazawar gwamnati

Arewa: Dan majalisa ya tura sako ga gwamnati

A baya kun ji cewa dan majalisa mai wakiltar Kura/Madobi/Garun Malam a majalisar wakilan Najeriya, Datti Umar Yusuf ya ce akwai bukatar gwamnatin tarayya ta gyara lantarkin Arewa.

Hon Datti Umar Yusuf ya caccaki hukumomin kula da harkokin lantarki na kasa da gaza samar da hanyoyin ko ta kwana na samar da wuta ga jihohin Arewacin Najeriya na sama da mako biyu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.