Kwana Ya Kare: Fitaccen Jarumin Fina Finan Najeriya Ya Rasu Yana da Shekara 101

Kwana Ya Kare: Fitaccen Jarumin Fina Finan Najeriya Ya Rasu Yana da Shekara 101

  • An yi rashin ɗaya daga cikin fitattun jaruman da ake ji da su a masana'antar fina-finai ta Yarbawa a Kudu maso Yamma na Najeriya
  • Fitaccen jarumi wanda ya daɗe a masana'antar, Pa Charles Olumo Sanyaolu wanda aka fi sani da Agbako ya yi bankwana da duniya
  • Marigayin wanda ya rasu da sanyin safiyar ranar Alhamis, 31 ga watan Oktoban 2024 ya bar duniya yana da shekara 101 da haihuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Masana'antar fina-finan Najeriya ta shiga jimami sakamakon rasuwar fitaccen jarumin nan, Pa Charles Olumo Sanyaolu, wanda aka fi sani da Agbako.

Pa Charles Olumo Sanyaolu ya yi bakwana da duniya yana da shekara 101 a duniya.

Jarumin fina-finan Najeriya ya rasu
Charles Olumo ya rasu yana da shekara 102 Hoto: mrlatin1510
Asali: Instagram

Jarumin fina-finan Najeriya ya rasu

Kara karanta wannan

TCN: Yadda yan bindiga suka hana gyaran wutar Arewa

Jaridar Tribune Online ta rahoto cewa fitaccen jarumin ya rasu ne da sanyin safiyar ranar Alhamis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Marigayin ya rasu ne lokacin da ya koma barci bayan ya yi ƙorafin cewa yana jin gajiya a tattare da shi.

Shugaban ƙungiyar TAMPAN, Bolaji Amusan, wanda aka fi sani da Mista Latin ya tabbatar da rasuwarsa a shafinsa na Instagram.

Amusan yana mai cewa iyalansa za su sanar da lokacin birne shi nan ba da jimawa ba.

Marigayin ya yi suna a fina-finan Yarbawa

Agbako wanda ya yi suna a masana’antar fina-finan Yarbawa, a yanzu ana tunawa da shi a matsayin jarumin da ya fi daɗewa a harkar wasan kwaikwayo.

Marigayin ya ɗauki tsawon shekaru sama da 100 a duniya kuma ya bar tarihi wajen bunƙasa al'adun Najeriya.

Marigayin ya yi tasiri a masana'antar fina-finan Yarbawa, inda ɗimbin masoya suka taso suna kallon wasan kwaikwayonsa a cikin fitattun fina-finan Yarbawa. 

Kara karanta wannan

Wani babban malami ya miƙa kansa ga ƴan bindiga, ya ceci ɗaliban da aka sace

Jarumin Nollywood ya rasu

A wani labarin kuma, kun ji cewa an shiga wani irin yanayi bayan sanar da mutuwar wani jarumin fina-finai a masana'antar Nollywood da ke yankin Kudancin Najeriya.

An tabbatar da mutuwar Otunba Ayobami Olabiyi a ranar Laraba 16 ga watan Oktoban 2024 a birnin Ibadan a jihar Oyo.

Marigayin da aka fi sani da Bobo B ya yi shura a masana'antar fina-finan Nollywood kuma ya taɓa riƙe muƙamin shugaban ƙungiyar TAMPAN.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng